Ballagaza: Karuwanci Da Rayuwar Karuwai A Legas

Wani bincike ne mai zurfi ne na irin ayyukan yawancin karuwan da ke garin Legas gari ma fi yawan mutane a nahiyar Afirka, binciken ya kuma haɗa da kawalai da ke haɗa karuwan da mazaje a Unuguwannin Ɓictoria Island da Lekki da Ajah da sauran wuraren da ake gudanar harkoki na masha’a Kaman kulub-kulub in da sukan daɗu da hulɗarsu. Karuwan kan samu gidaje a unguwanni masu tsada inda sukan kama haya su biyu ko uku a a ɗaki, kuma sun samu ƙwarewa ta musamman na yaudarar manyan masu kuɗi a wuri tatrurrukan aure kona “Birthday” da ire-iren su domin samun masu neman hulda da su. LEADERSHIP A Yau ta gano cewa ɗaukar irin waɗannan matan na tsawon dare yana kamawa ne daga N30,000 zuwa N50,000 hakan ya kuma danganci wuri da waɗanda suka haɗa “Harkar” matan ne kan zaɓi wurin da za a yi “harkar” saboda dalilan tsaro in an cimma inda za a haɗu, matan kan zaɓi zuwa wurin “Haɗuwar ne a motar hawansu ko kuma a wasu motocin haya masu tsada wanda akasari suna da mambobin wayar direbobin, hakan, in...