Kuskure tara(9) Da Ma’aurata Kan Yi A Yayin Jima’i

Akwai abubuwa da yawa wadanda Ma’aurata suke aikatawa alokacin Jima’insu. Kuma wadannan abubuwan suna da illoli masu yawa dangane da lafiyarsu jikinsu ko addininsu. Ga wasu ‘yan kadan Zan lissafo: 1. Rashin gabatar da wasanni kafin Jima’i : wannan ba daidai bane domin kuwa Manzon Allah (saww) yace “IDAN ‘DAYANKU YAYI NUFIN KUSANTAR IYALINSA, TO LALLAI ASAMU ‘DAN AIKE ATSAKANINSU”. Sai Sahabbai suka ce “Wanne irin ‘dan aike?” Sai yace “SHINE SUMBA (KISS) DA KUMA MUBASHARA (RUNGUMAR JUNA). Rashin gabatar da irin wadannan wasannin yakan haifar da rashun gamsuwar Jima’i. Shi kuwa rashin gamsuwar Jima’i yakan haifar da matsalolin da zasu kawo rabuwar auren. Yana daga cikin fa’idodin gabatar da wadannan wasannin, Zai sa Maniyyin ita Macen ya gangaro daga ainihin inda yake, sannan kuma zata samu cikakkiyar gamsuwa. 1. KUSKURE NA BIYU SHINE TSOTSON AL’AUR JUNA: Mun sha amsa tambayoyi akansa ana Zauren Fiqhu, kuma mun ce wannan kuskure babba wanda ko dabbobi basu yinsa. Shi baki dan Adam anyi...