Shugaban Riko na Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa ‘yan siyasa da ke ficewa daga wannan jam’iyya zuwa waccan, ba alamomi ba ne da ke nuna cewa sun tsere wa EFCC daga gurfanar da duk wani cikin su wanda ya wawuri dukiyar gwamnati. Da ya ke jawabi a wurin wata ganawar musamman da ya yi da editocin wasu jaridun kasar nan a Lagos, Magu ya ce babu wurin buya ga irin wadannan ‘yan siyasa, ballantana su fake daga kamu da, bincike da kuma gurfanarwar da EFCC za ta yi musu. “Kotu ce kawai za ta iya wanke mutun daga zargin ko ya ci kudi ko bai ci ba. Idan ya ci za ta hukunta shi, idan bai ci kudi ba kuwa, za ta sallame shi.” Da ya ke maida martani daga wata tambaya da aka yi masa cewa jam’iyyar APC mai mulki na yin katsalandan a cikin aikin EFCC, Magu cewa ya yi, bai taba samun wani umarni ko koron yin wata alfarma kan wani bincike ya hukumar sa ke yi ba. Magu cewa ya yi abin ya zama tamkar al’ada ga ‘yan siyasa idan ana binciken su sai su rika cewa ana yi musu bi-ta-da-kulli na siyas...