Yadda ‘Yan Jarida Tare Da Hadin Gwiwar Gwamna Bagudu Suka Gano Maboyar Giwaye Biyu A Dajin Ganten Tudu Ta Jihar Kebbi

A kwanannan ne rahotanni ke fito wa daga karamar hukumar mulki ta KoKo-Besse da ke a cikin jihar Kebbi cewa, “An samu labarin garin wasu giwaye a fadamar garin Zariyar Kalakale, inda daga nan ne jama’ar yankin suka fara tattaki zuwa cikin fadamar garin nasu domin gane wa idanun su wadannan giwayen da suka shigo cikin yankin nasu. Bayan jama’ar garin na Zariyar Kalakala sun ganar wa idonun su wadannan giwayen sai labari ya fara zagayawa cikin al’ummar jihar da kewayenta. Haka kuma shuwagabannin karamar hukumar da kuma sarakunan gargajiya na yankin suka samu wannan labarin ganin giwaye a yankinsu, daga nan ne shuwabannin suka sanar da gwamnatin jihar ta hannun kwamishinan ma’aikatar kula da muhalli ta jihar, Alhaji Musa Hassan Kalgo wanda a nan take ma’aikatar sa ta dauki matakin sanar da Gwamnan jihar, Sanata Abubakar Atiku Bagudu domin daukar matakin sanar da hukumomin da abin ya shafa na jihar da kuma na gwamnatin tarayya. Haka kuma kafin Gwamnan jihar ya kai ziyarar gani da ido an s...