Posts

Tirkashi: Zpretty ta caccaki 'yan soshiyal midiya

Image
Matashiyar jarumar masana’antar Kannywood , Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zpretty ta caccaki ma’abota tsegumi a kafafen sada zumuntar zamani - Jarumar ta wallafa bidiyo a shafinta na Instagram ne inda ta ke magana a kan masu bata wa jaruman masana’antar suna - Ta yi gargadin cewa, zata iya daukar mataki a kan duk wanda ta kama da laifin bibiyar lamurranta tare da bata mata suna Matashiyar jarumar masana’antar Kannywood, Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zpretty ta caccaki ma’abota amfani da kafafen sadarwa ta zamani. A wani bidiyo da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, ta yi suka ga wadanda suka kware wajen bibiyar lamuranta da na sauran jarumai abokanan sana'arta. Wadanda daga zarar sun ga jarumi ko jaruma ta wallafa sabon hoto, zasu fara yadawa tare da tsokaci a kai. Jarumar ta yi kausasan kalamai na musamman ga masu wallafa bayanai a dandalin YouTube, inda ta ce mafi yawansu basu da aikin yi face shirya karya da gulma, don batawa jaruman masana’antar Kannywoo

Dadewa wajen Jima’i ba ya sa a haifi da na miji – Likita

Image
Wani likita da ya kware a harkar duba lafiyar mata mai suna Olatoye Ogundipe ya bayyana cewa daukar tsawon lokaci a wajen jima’i da yadda ake saduwa ba shine ke sa a haifi mace, namiji ko ‘yan biyu ba. Ogundipe ya fadi haka ne da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Ilori jihar Kwara. Ya ce mutane da dama na yawan cewa idan namiji na yawan saduwa da iyalinsa ko kuma yana dadewa a lokacin da ake saduwa da iyalinsa shine zai sa a haifi da namiji ko kuma ‘yan biyu maza. “Wasu mutane na ganin saduwa da mace da rana na sa a haifi ‘ya’yan da suke da nakasa, wasu kuma na ganin cewa mace za ta haifi namiji dake da koshin lafiya idan mijinta ya sadu da ita bayan ta gama jinin haila. Ogundipe yace duk ire-iren wadannan bayanai shafa labari ne. Haihuwan ‘ya’ya ya danganta da yadda kwayayen halittar mace da na miji suka garwaye ne. “ Kwayayen halittan da ke dauke a cikin maniyyin namiji shine ke sa a haifi da namiji ko kuma ‘ya mace. Idan kwan hallita X ya gamu da na mace X a l

Harkar fim ce ta sani nake yin shigar mutunci a gari - Fati Shu'uma

Image
Daya daga cikin fitattun jarumai mata da suke tashe a wannan lokacin, Fati Shu’uma, ta bayyana yadda harkar fim ta canza mata rayuwarta - Ta bayyana cewa, fim ya taimaka wa rayuwarta , ta yadda ko fita za ta yi sai ta yi shiga ta mutunci - Jarumar ta bukaci addu’ar masoyanta a kan cikar burinta na samun miji nagari wanda zasu zauna lafiya tare da fahimta juna Daya daga cikin fitattun jarumai mata da suke jan zarensu a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Fati Abubakar, wacce aka fi sani da Fati Shu’uma, ta bayyana harkar fim a matsayin wata harka wacce ta sauya mata rayuwa ta zama wata ta daban. Wanda da kamar ba a harkar fim take ba, da zai kasance ba haka lamarin yake ba. Jarumar ta fadi haka ne a lokacin tattaunawarta da jaridar dimokaradiyya dangane da halin da ta samu kanta a a cikin masana’antar ta Kannywood. Jarumar tace: “Gaskiya na samu sauyin rayuwa, wanda da kamar ba fim nake ba to hakan ba zai kasance a gareni ba, don ka ga zan iya shiga ko ina kuma in yi ma’amala da jama’

(Bidiyo) Adam a zango ya shigar wa jaruma mai kayan mata fada

Image
Adam a zango ya shigar wa jaruma mai kayan mata fada Jarumin ya baiyana cewa kwana2 baice komaiba Amma yauwa zaiyi magana akan jaruma ga Abinda yake fadi a kasa

'Kokarin kwaikwayon Turawa ya sa ake yawan sukar 'yan Kannywood'

Image
Jama'a da dama na yawan sukar taurarin fina-finan Hausa wato Kannywood musamman a kafofin sada zumunta. Akwai wasu daga cikin 'yan masana'antar Kannywood din da ba a cika sukar su ba, wadansu kuma a duk lokacin da suka yi magana, wasu kan yi kokarin sukar su. BBC ta tattauna da Ibrahim Sheme, dan jarida ne kuma masani kan harkar fina-finan Hausa kan yadda yake kallon wannan lamari. Ya bayyana cewa akasari caccakar da ake yi wa 'yan Kannywood na da alaka da irin sakonnin da suke wallafawa a shafukansu na sada zumunta, amma kuma a wani lokacin, akwai nau'in wasu mutane da ko wane irin sako suka wallafa sai sun caccaki 'yan Kannywood din, in ji Ibrahim Sheme. Ya bayyana cewa ''akwai fadace-fadace da rigingimu da 'yan fim suka rinka shiga ciki wanda wannan ya ja musu bakin jini." Sheme ya kuma ce a wani lokacin wasun su kan fadi wata magana wacce za ta jawo ce-ce-ku-ce wanda daga baya har ya ja a rinka zaginsu. Har ila yau ya bayyana cewa "a sh

Bidiyo: Allah Ya Tona Asirin Wasu Mazinata, Yayin Da Mazakutar Namijin Ta Makale Jikin Macen Bayan Sun Gama Lalatar Su

Image
Asirin wasu mazinata ya tonu yayin da suka makale a jikin juna bayan sun kammala lalata a wani otel – Bayan sunyi sunyi su rabu sun kasa sai suka fara ihun neman taimako, inda mutane suka dauke su zuwa wajen wata bokanya domin ta raba su – Wannan lamari dai ya faru a wani otel ne dake tsakiyar kasuwa, inda mutane suka yi dafifi domin kallon ikon Allah Wani mutumi ya makale tsakanin kafafuwan wata mata bayan sun gama aikata lalatar su a wani dakin otel dake kusa da wata kasuwa a kasar Kenya. Jaridar Nairobi News ta ruwaito mutanen sun fara ihun neman taimako ne bayan namijin yayi yayi ya kasa cire mazakutar shi daga jikin macen. An dauki mutanen an kai su wajen wata mata mai maganin gargajiya, bayan mutane sunyi iya yin su sun kasa raba su. Wanda lamarin ya faru a kan idon su sun ce, matar mai suna Sabina Moraa, dama can ana zargin ta wannan halayya ta bin maza duk kuwa da cewa tana da aure, hakan ya sanya mijinta yaje neman magani a wajen boka domin ya ganewa kanshi da idon shi. Bokan

Kakkausan lafazi: Minista Pantami ya yaba ma Hadiza Gabon kan neman gafarar Allah da ta yi

Image
Ministan Sadarwa na Najeriya kuma shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Isa Ali Pantami ya yaba ma fitacciyar jarumar Kannywood, Haliza Aliyu Gabon akan wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter. A cikin rubutun, an gano jarumar na neman yafiyar Allah akan wani kakkausan martani da ta mayar wa da wani ma’abocin shafin Twitter bayan ya zarge tad a aikata zina. Da fari dai jarumar ta mayar masa da zazzafan martani inda tace shakka babu da mahaifinsa ta yi zinar. Sai dai kuma bayan dan nazari da sharhi da mabiyanta suka yi, Hadiza ta fito ta bayar da hakuri inda ta nemi yafiyar Allah. Hakan da jarumar ta yi ya burge mutane da dama ciki harda Sheikh Pantami, inda ya mayar mata da martani tare da fatan Allah ya cigaba da karewa da kuma yafewa. Pantami ya jaddada cewa shakka babu Allah na son duk wanda ya yi kuskure kuma ya gane hakan sannan ya nemi yafiyarsa. Ga yadda ya wallafa a shafin nasa: " Wannan babban abun a yaba ne a nemi gafarar Allah bayan yin wani kusku