Dan Takarar APC Ya lashe zaben gwamnan Ondo
Hukumar zaben Najeriya ta ayyana dan takarar gwamnan
jihar Ondo a karkashin jam'iyyar APC a matsayin wanda ya
lashe zaben jihar da aka yi ranar Asabar.
Rotimi Akeredolu ya samu kuri'a 244, 842, yayin da mutumin da
ke biye masa, dan takara a karkashin jam'iyyar PDP, Eyitayo
Jegede ya lashe kuri'a 150,380.
Babban baturen zaben jihar Farfesa Ganiyu Ambali, wanda ya bayar
da sakamakon zaben, ya kara da cewa mutum 1,647, 976 ne suka
kada kuri'unsu.
Rotimi Akeredolu zai karbi mulki ne daga hannun Olusegun Mimiko
na jam'iyyar PDP, wanda ya kwashe shekara takwas a kan mulki.
Zaben na jihar Ondo ya ja hankalin 'yan Najeriya sakamakon kai
ruwa ranan da aka rika yi tsakanin jiga-jigan manyan jam'iyyun biyu
da ma masu son tsayawa jam'iyyun takara gabaninsa.
Yanzu dai jiha daya ce kadai ta rage a hannun jam'iyyar da ba
APC ba a yankin kudu maso yammacin Najeriya, wato jihar Ekiti.
Comments
Post a Comment