Fara Karbar Haraji Daga Masu Buga Wayar Salula A Najeriya
Gwamnan babban bankin Najeriya ya baiwa gwamnati
shawarar duba yiwuwar fara karbar haraji daga masu buga
wayar salula da ya haura mintuna uku, domin samun kudin
shiga.
Godwin Emiefele, gwamnan babban bankin Najeriya yace idan aka
samu nasarar kaddamar da hakan kasar zata samu kudin shiga
kimanin Naira Biliyan Dubu 100 a shekara. Sai dai yace wannan
mataki ba zai shafi masu karamin karfi ba, domin kuwa za a rika
cajar harajin ne daga wadanda suka buga wayar da ta haura minti
uku kacal, wanda kuma yace dawuya a samu talakan dake buga
waya sama da mintuna uku.
Wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka ya zanta da wasu ‘yan
Najeriya a jihar Lagos, yayin da wasu ke ganin yin hakan ba zai
takura ba, wasu kuwa na ganin wannan wata hanyar zalunci ce ga
talaka domin akwai hanyoyi masu yawa da yakamata gwamnati ta
mayar da hankali akai maimakon ta kiran waya.
A cewar gwamnan dai, gwamnati zata iya samun Naira Biliyan 100
a karshen kowacce shekara, a harajin da zata cire a kudaden da ake
buga wayar salula a hannun jama’a. Najeriya dai na daya daga cikin
kasashen duniya dake da yawan masu buga waya, abin da ke
kawowa kamfanoni masu zaman kansu dake samar da wayar
makurdan kudaden shiga.
Gwamnati dai ta rasa wadannan kudade ne sakamakon cefanar da
kamfanin waya na kasa NITEL a shekarun baya. Yanzu dai abin
jira a gani shine ko ‘yan Majalisa da ita kanta gwamnati da kuma
talakawa ko zasu amince da wannan shawara ta gwamnan babban
bankin Najeriya.
Comments
Post a Comment