Abubuwa 10 Da Muke Yi Kuma Kowannensu Yana Warware Imanin Mutum

Abubuwa 10 Da Muke Yi Kuma
Kowannensu Yana Warware Imanin Mutum

Daga Malam Aminu Daurawa
A wannan 'yar gajeruwar
fadakarwa fitaccen Malamin
Addinin musulunci, Sheikh Aminu
Ibrahim Daurawa ya zayyano
mana wasu abubuwa 10 da
kowanensu ke warware imani kuma
galibin mutane sun shagaltu wajen
aikatasu.
1. Shirka da kashe-kashenta.
2. Halasta haram ko haramta halal
da gangan.
3. Inkarin wani rukuni a addinin
musulunci.
4. Wulakanta aya ko hadisi ko yin
izgili da su.
5. Sukan wani Annabi daga cikin
Annabawa ko rashin yarda da su.
6. Kyamar wani abu daga cikin
koyarwar musulunci.
7. Kin yarda da Kur'ani ko
ingantattun Hadisai.
8. Yin tsafi da halasta shi.
9. Nuna soyayya ga kafurai ko
goyon bayansu akan kafurci.
10. Fifita wata shari'a ko wata
doka akan ta Allah da Annabi
S.A.W bisa son rai da yarda.
ALLAH YA TSARE MANA IMANIN
MU.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15