Kalli sabon bidiyon da bokoharam ta saki na ma'aikatan hako mai


Download it here

Kungiyar Boko Haram bangaren Albarnawi ta saki wani bidiyo da ke nuna mutane uku da ta ce ta kama lokacin wani harin sunkuru da ta kai wa ma'aikatan hakar mai a jihar Bornon Najeriya.
Bidiyon wanda gidan talbijin na Channels a Najeriya ya ce an aike masa, ya nuna mutanen uku zaune sannan bayansu akwai wani kyalle.
Biyu daga cikin mutanen sun ce ma'aikatan sashen kimiyyar kasa ne na jami'ar Maiduguri, a inda shi kuma na ukun ya ce shi direba ne.
Mutanen dai sun nemi gwamnati da ta kai musu dauki.
A ranar Talata ne dai ake zargin kungiyar Boko Haram ta abka wa wata tawagar ma'aikatan aikin hakar man fetir da ke tafe cikin rakiyar sojoji da 'yan sintiri.
Kuma yawancin ma'aikatan sun fito daga jami'ar Maidguri ne, duk kuwa da cewa akwai ma'aikatan kamfanin mai na kasar wato NNPC.
Kamfanin na NNPC dai ya ce wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun sace masu binciken mai guda goma da suke masa aiki a jihar Borno.
Sai dai sojojin Najeriya sun ce sun ceto wasu daga cikin mutanen al'amarin da har ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji guda tara.
Rahotanni sun nuna cewa sakamakon kwantan baunar da kungiyar ta kai mutane fiye da 40 ne suka mutu da suka hada da sojoji da 'yan sintiri.

Sauke bidiyon anan

©Nairaland

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15