Mai son duniya baya barci- inji aliko dangote

Aliko Dangote yace a kowace rana ya kan yi aiki har na sa'a 18. Tun karfe 8:30 na safe Dangote yake shiga Ofis kuma ba zai fito ba sai bayan awa 18. Wannan dai ya bi jikin sa don kuwa bai fi yayi barci awa uku tak a raba ba. 

Dangote yace ya kan tashi tun karfe 5:00 na asuba bayan yayi sallah sai ya shiga atisaye inda yake motsa jiki da tafiya ta kilomita 10. Mike Adenuga ya taba ba Dangote shawara yanzu ya kamata fa ya rika runtsawa don shekaru sun zo. Duk Afrika dai babu wanda ya kama hanyar arzikin Dangote wanda ya mallaki sama da Dala Biliyan 16. Dangote na da ma'aikata sama da 26,000 a harkar noma, abinci, mai, kayan gini dsr.

Read more: sabon bidiyon da bokoharam ta saki na ma'aikatan hako mai da Jamian University of maiduguri

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15