[Tarihi] Kalli jerin mutanen da aka kashe sa'adda aka yi ma Sardauna juyin mulki (Hotuna)


A yau an kwashe sama da shekaru 52 da suka gabata kenan da bindige gamji dan kwarai, Firimiya na farko kuma daya tilo na yankin Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato. Sir Ahmadu Bello ya kwanta dama ne a ranar Juma’a, 15 ga watan Janairu cikin watan Azumi na shekarar 1966, shekau shidda da samun yanci, inda wasu kananan hafsoshin soji suka far masa a daren juma’an suka yi masa ruwan harsasai.  Manjo Chukwuemeka Kaduna Nzeogwu, wanda ya jagoranci kai harin ya bayyana dalilansa na kashe Sardauna; da suka hada da girman kai, cin hanci da rashawa, son kai, da kokarin kaddamar da jihadi a Najeriya. Sai dai an tabbatar gaba daya wadannan dalilan daya dogara akansu duk shaci fadi ne, don kuwa ko bayan da aka kashe Sardauna, an tarar da Banki na binsa bashi ne ma, maganan son kai kuwa, ai a wancan lokaci kowane yankin kasar nan kokari take ta gina jama’anta da yankinta. Wani na hannun daman Sardauna, Sheikh Abubakar Gumi ne da kansa ya fada ma Manjo Nzeogwu karya yake yi game da zargin Sardauna da yake na kokarin kaddamar da jihadi, inda Shehin Malamin ya fada masa Sardauna bai taba tara makamai a ko ina ba don shirin yaki. Manya cikin wadanda aka hallaka a wannan rana, a cikin mutane 22, sun hada da Firai ministan Najeriya, Abubakar Tafawa Balewa, Firai ministan yankin yammacin kasar nan Samuel Akintola, janar Zakari Mai Malari, Ademulegun, Ahmad Ben Musa, Yakubu Pam, Largema, Kur Muhammad. Ga jerin sunayen mutanen da aka hallaka nan: Ahmadu Bello Sardauna Abubakar Tafawa Balewa
-naijhausa

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15