Yadda yan sanda suka Kama jaruma Nafisa Abdullahi a katsina

Babban Forudusa Jamilu Ahmad Yakasai (Dakan-daka) ya sa 'yan sanda sun kama Nafisa Abdullahi da talaitainin dare a katsina., suka dauko ta zuwa birnin kano Inda suka aje ta a bayan kanta na tsawon lokaci. In ba don maslahar da aka yi ba to da yanzu an garkameta a gidan yarin Kano...
Sabani ya shiga tsakanin jarumar da furodusan sakamakon jingine aiki fim din sa mai suna "Mutuwar Aure" da ta yi ana tsakar yi ba tare da wani dalili da ta sanar dashi ba. Sai aka shiga wasan buya tsakanin sa da ita. A cewar Jamilu ya bi duk wasu hanyoyi don a samu maslaha amma jarumar ta bijire daga karshe dai ya maka ta kotu yana neman ta biya shi diyyar asarar da ya yi.
A ranar da aka yi zaman kotun Nafisa ba ta je ba, kuma bata aika da wani uzuri ba, don haka ya lashi takobin cewa sai ya nuna mata cewa shima ba Kanwar lasa bane ba.
Kwatsam sai suka labarin jarumar za ta bayyana a wani wasan gala da aka shirya yi a Katsina don haka kuma Nafisa za ta je wasan.
An gama wasan cikin hikima suka gano otal din da ta sauka, suka je suka kamata wajen karfe 11 na dare yan sandan suka taso keyar ta zuwa birnin Kano. Suka wuce da ita hedikwatar 'yan sanda shiyya ta 1, (Zone 1) bayan ta wayi gari Lahadi sai aka shirya cewa za a kai ta kotu ranar litanin.
Sai wasu daga cikin 'yan fim irin su Ali Nuhu, Adam Zango, Dauda kahutu Rarara, su ka shiga maganar sai ta bada hakuri kuma tace za ta karasawa Furodusan aikin sa kamar yadda aka tsara tun farko.
Yanzu dai an samu maslaha har ta ida masa aikin fim din mai suna "Mutuwar Aure

©rumbun Kannywood

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15