An gano su waye ke shigo da makamai Najeriya
Hameed Ali, yace mutanen uku suna amfani da adireshin "Ayogu Cyril, Ayogu kelvin da Ayogu Great James" dake wata unguwane a cikin birnin tarayya, Abuja, da kuma unguwar Bariga a cikin Jihar Legas. Wasu mazaunan unguwar sunce baza su iya san sana'ar shi mista Ayogu ba, kuma basa tunanin yana da wani kamfanin man fetur illa dai sun san shi dan kudu ne kuma sunanshi na gaskiya ba James Ayogu ko Cyril Ayogu bane. A cikin zantawar da akayi da wani makobcinshi da ya bukaci a boye sunan shi yace, "Kelvin ya zauna a nan kuma ya bar nan kimanin shekaru biyu da suka wuce amma yanzu bamu san inda ya koma da zama ba".
A ranar Alhamis da ta gabata hukumar hana Fasa kwabri ta ce mutanen na amfani da wata irin kwantena da na'urar su ba ta iya fada masu abin da ke ciki. Ya kara da cewa makamai 470 da suka samo sai da suka bukaci binciken cikin kwantenar mai lamba CMAU189817/8 kafin su samu nasarar kama makaman. Hamid Ali yace zamu zanta da hukumar kasar Turkiyya akan yadda ake Shigo da makamai daga kasar zuwa Najeriya domin ko a watanni 8 da suka gabata hukumar hana fasa kwabri ta kama akalla makamai 2,671 kuma duka daga kasar Turkiyya. Kuma yace suna nan suna binciken dalilin da yasa ake safarar makaman zuwa kasar Najeriya.
-Hausa.naij.com
Comments
Post a Comment