Bajinta 9 da Buhari ya yi cikin mako guda


A wannan makon da ya gabata kadai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bajintai daban-daban wadanda ya sanya ko ma su sukar shi sun yaba. Wannan bajinta da shugaban kasar na Najeriya ya yi sun cancanci yabo domin kuwa abubuwan da ya yi har ta a kasshen ketare maganganun shugaban kawai ke gudana a bakunan mutane.
Irin wannan bajinta da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, ya sanya kasashen ketare sun kara ganin kima da mutuncin kasar Najeriya da shi kan sa shugaban. Wasu da dama su na ikirarin cewa shugaba Buhari shine shugaban nahiyyar Afirka, musamman idan aka yi la'akari da irin jawabai da ya yi a makon da ya gabata a taron majalisar dinkin duniya. Ga jerin bajintai 8 da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi cikin mako guda kacal
1. Shugaba Buhari ya bayar da umarnin sakin basussuka na kudi har Naira Biliyan 290 da ma'aikatan gwamnatin tarayya suka biyo tun a shekarar 2007. 

2. Buhari ya koma baya zuwa shekarar 2003 domin biyan Naira Biliyan 45 na kudin ajiye aiki na ma'aikatan hanyoyin jiragen sama na Najeriya, wato Nigerian Airways. 

3. Karfin wutar lantarki na Najeriya ya hobbasa har zuwa ma'auni 7001 na megawatts 

4. Shugaban kasar ya samo motocin yaki na zamani har guda 200 daga kasar Jordan domin ci gaba da kulawa da harkokin tsaro a kasar nan. 

5. Kungiyoyin ASUU, NASU, SSANU, ULC da kuma kungiyar likitoci sun janye yajin aikin su sakamakon yarjejiniya da suka gudanar da gwamnatin ta Buhari. 
 
Ga jerin lambar yabo da jinjina da shugaba Buhari ya samu daga idon duniya 

1. Tsohon sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon ya cewa Buhari: "Shugabannin duniya gaba daya su na girmama ka, ciki har da ni. Sanadiyar ka kasar Najeriya ta kara kima da mutunci a idon duniya". 

2. Kamfanin dillancin labarai na kasar Amurka wato CNN ya bayyana shugaba Buhari a matsayin shugaban nahiyyar Afirka gaba daya. 

3. "...Zan so a ce shugabannin Afirka gaba daya kamar shugaba Buhari suke..." sako daga shugaban kasar Amurka Donald Trump. 

4. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na daya daga cikin shugabannin duniya 10 da ake ta tofa albarkatun bakuna a kai a birnin New York na kasar Amurka, sakamakon taron majalisar dinkin duniya da aka gudanar a mokn da ya gabata.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15