Dalilin da ya sa nake damuwa da Nigeria – Bill Gates


Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Bill Gates, ya ce Najeriya tana daya daga cikin kasashen da yake sanya ido kansu sosai. Bill Gates wanda ya bayyana haka a wata hira da BBC, ya ce kasar tana da muhimmanci ne a wurinsa saboda ita ce ta fi kowace kasa yawan al'umma a nahiyar Afirka. "Wannan ne ya sa gidauniyarta ta Bill & Melinda Gates Foundation take ci gaba da aikace-aikacenta a can," kamar yadda ya ce. Har ila yau, ya ce akwai babban kalubale a fannin kiwon lafiya a yankin arewacin kasar. "Akwai matsalar cutar maleriya da kuma batun 'yan gudun hijira. Muna aiki da wadansu daga cikin gwamnatocin jihohi kamar na Kano da Borno a kokarinmu na ganin mun magance kalubalen kiwon lafiya a yankin," in ji shi.
Ya ce ayyukan gidauniyarsa suna taimakawa wajen rage mutuwar mata masu juna biyu da kuma kananan yara a fadin kasar. Sai dai ya ce suna aiki ne tare da gwamnatin kasar da kungiyoyi masu zaman kansa da kuma attajirin nan da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote - wanda dan kasar ne. Kamar sauran kasashen Afirka, Najeriya na daya daga cikin kasashen da aka fi yawan samun mace-macen mata wajen haihuwa da kuma na kananan yara.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15