jerin sunayen makarantun kudi 10 mafi tsada a Najeriya, da kudin da suke chaja
Yanzu shekara ta zagayo da iyayen yara zasu fara neman makarantun da suka yi fice wajen bada nagartacccen ilimi. A wannan rahoton
Hausazone.com ta kawo muku jerin fitattun makarantun sakandire da suke bada ingantaccen ilimi
10. Loyola Jesuit, Abuja Makarantar Loyola Jesuit, makarantar kwana ce da aka bude ta a shekarar 1996. Makarantar an kafa ta ne a garin Abuja a kan titin Karu-Karshi, Gidan Mangwaro. Kudin makarantar dalibi daya yana kamawa N2.8m, kuma a lokacin neman daukan dalibai makarantar na da zabi wanda yake wa wasu iyayen wahala wajen saka ‘ya’yansu. Tana bada ingantaccen ilimi sosai wanda yake jawo hankalin iyaye da yawa.
9 Meadow Hall, Lagos Misis Kehinde Nwani ta kafa makarantar a 2002 a garin Legas a titin Elegushi Beach Road, Lekki wanda kudin makarantar dalibi daya yana kamawa N3m a shekara.
8. Greensprings School, Lagos Makarantar na nan a lamba 32, Olatunde Ayoola Avenue a jihar Legas. Ta kunshi bangaren kwana da jeka ka dawo, kudin dalibi daya na 'yan kwana na kamawa sama da N3m a shekara na dan jeka-ka-dawo kuma N1,925,200m a shekara
7. Whiteplains British School, Abuja Makaranta ce da tayi fice a wajen samar da ilimi irin tsari na kasar Birtaniya, kudin makrantar kuwa a shekara yana kamawa N3.5m a shekara. Makarantar na nan a Obafemi Awolowo Way, Jabi, Abuja
6. Day Waterman College, Abeokuta Makarantar sakandire ce ta kwana da ke titin Asu Village Road a garin Abeokuta a jihar Ogun. Kudin makarantar kuwa a shekara ana biyan N3.7m.
5. Lekki British International high School, Lagos An kafa makarantar a shekarar 2000 da asalin tsarin karatu irin na turawa, tana daya daga cikin manyan makarantu da ke samar da ingantaccen karatu a fadin yankin Afirka maso yamma. A shekara ana biyan kudin dalibi daya kimanin N4m a cikin kudin har da na abinci da litattafai da kayan inifom da na sawar lahadi a cikin makaranta.
4. American International School, Abuja Wadda ke Durumi a garin Abuja, an kafa ta tun 1993 da tsarin karatu na kasar Amirka wadda dalibai iri-iri na wasu kasashen ma suna halartar makarantar. Daliban da ke cikin makarantar bas u fi 500 ba saboda tsadar ta har N4.3m.
3. British International School, Lagos An kafa ta a Satumba 2001 a Muri Okunola Street, Victoria island, Legas, mai dauke da filin wasa na yara dakin waka, tiyata na wasan kwaikwayo, dakin ruwa na iyo. Iyayen yara na biyan kudin makarantar da dalar Amurka ne wanda a yanzu yake kamawa N4.48m a kudin Najeriya.
2. Grange High School, Lagos Tana cikin manyan makarantu da suka fi tsada a Najeriya, da kudin makaranta N4.5m. Tsarin karatun makarantar na tsarin turai ne, makarantar na garin Legas a lamba 6 Harold shodipo Crescent, Ikeja.
1. American International School, Lagos Kafin tsarin makarantar yana bi da tsarin karatun Amirka ne, kudin makarantar ma kadai ba a biya sai da kudi na dalar Amurka,
Comments
Post a Comment