SANATA KWANKWASO ZAI GINAMA YAN GUDUN HIJIRA GIDAJE GUDA 370 A BORNO


SANATA KWANKWASO ZAI GINAMA YAN GUDUN HIJIRA GIDAJE GUDA 370 A BORNO ....Sunan Birnin kwankwasiyya model city Tun a jiyane Jirgin Jagoran Kwankwasiyya ya sauka a Birnin Maiduguri na jihar Borno domin gabatar da ziyarar aiki ta Kwana daya a waccar jihar da rikicin Boko Haram ya Daidaita. A yau Lahadi 1 24/09/2019 Sanata Kwankwaso yayi jaje tare da nuna alhini ga jama'ar Borno bisa iftila'in rikicin Boko Haram da sukasha fama dashi a wannan gari nasu Wanda yayi sanadiyar janyo asarar rayuka da dukiyoyin da bazasu lissafu ba. A yau din dai sanata Kwankwaso ya halarci bikin Saukar karatun Alkur'ani maigirma a Makarantar Darussalam Science & Islamic Academy. Sannan Sanata Kwankwaso a yau dinne dai yaKaddamar da bikin gina gidaje kaso na farko na zamani guda 370 Wanda akayiwa lakabi da "KWANKWASIYYA MODEL CITY" kuma za'a gina wayannan gidaje a rabasu ga mabukata kyauta ga wayanda rikicin Boko Haram ya rabasu da gidajensu. Kowanne gida zai kasance yana dauke da dakunan kwana guda 3, kuma za'ayi wannan gini a kuma yi bukin budesu cikin gaggawa domin bawa mabukata, za'ayi wannan gini ne a gefen titin Maiduguri zuwa Gamboru Ngala a guri Mai kallon Tashar mota ta Muna a birnin Maiduguri. Bayan kaddamar da wannan birni, Sanata Kwankwaso ya kamo hanyarsa ta dawowa Abuja.
Mikiya hausa

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15