YADDA AKA KASHE SIR AHAMADU BELLO SARDAUNA SOKOTO


YADDA AKA KASHE SIR AHAMADU BELLO SARDAUNA SOKOTO A KAN IDO NA, Inji Direban Sardauna: WATO ALHAJI ALI SARKIN MOTA: KOWA YA DAURE YA KARANTA DON KARIN ILIMI NE: Alhaji Ali Sarkin Mota shi ne ya zan ta da Wakili Jaridar Leadership yadda aka kashe Sir Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto Firimiyan Jihar Arewa akan idonsa. Ya shaidawa Jaridar cewar zan iya mantawa da komai, amma banda yadda sojoji suka kashe Sardaun da iyalin sa a gaban ido na a 15 ga watan Janairun 1966. Yasir Ramadan Gwale Ne Ya Fassara Daga Jaridar Leadership Ta Yau Leadership: Kana gidan Firimiya a ranar 15 ga watan Janairun 1966. Me zaka iya tunawa da ya faru a wannan ranar? Sarkin-Mota: Ga wadan da suke zaune a Kaduna zasu shaida yadda sojoji suke yin atisaye a makarantar Kafital dake unguwar Malali a garin Kaduna, duk lokacin da za ayi wani biki a hukumance. Amma a lokacin da ake shirin yiwa Sir Abubakar Tafawa Balewa Prime minister da Firimiya juyin mulki a 15 ga Janairun 1966 mun ga sojoji suna yin atisaye ba tare da wani biki ya gabata ba na hukuma. A ranar Juma'a 14 ga watan Janairun 1966, wani abokin aikina ya sanar da ni cewar, muna sa ran yin bakin alfarma a wannan rana daga Yammacin Najeriya zasu kawowa Firimiya ziyarar bangirma. Sai daga baya aka tabbatar min da cewar Cif Samuel Akintola, shi ne zai kawo ziyara Kaduna, a wannan rana, an shaida mana cewar zai sauka a filin jirgin sama na Kaduna da Misalin 11:30 na safe, dan haka ne muka shirya na tuka Sardauna zuwa filin jirgi shi da 'yan tawagarsa da Ministocinsa domin taryen Samuel Akintola. Mun isa filin jirgi, muna zaune a zauren manyan baki, muna jiran saukar jirgin da ke dauke da su Akintola, sai Firimiya ya duba agogonsa yaga lokaci ya nuna 12:00 na rana, daga nan ne Firimiyan ya aiki daya daga cikin Ministocinsa akan, yaje ya samu masu lura da sauka da tashin jirage ya tambaye su, me ya faru aka samu jinkirin saukar jirgin su Akintola, dan aiken yana zuwa suka shaida masa cewar, rashin kyawun yanayi ne ya hana jirgin sauka a kan lokaci, amma zai iso nan da 12:30. Muka cigaba da zama muna jira har 12:30 tayi babu alamun saukar wani jirgi, Firimiya ya kuma aikawa a tambayi ma'aikatan, shin ya akai har yanzu jirgin bai sauka ba, suka sake shaida masa cewar rashin kyawun yanayi ne ya janyo tsaiko, amma jirgin zai iso nan da 1:00, muna zaune har agogo ya nuna, karfe daya babu alamun saukar wani jirgi, aka kuma cewa, muyi hakuri Jirgin zai sauka karfe 1: 30. Daga nan ne, Firimiya ya tashi zai fita tunda yake Juma'a ce ranar dan zuwa Masallaci, sai ya gayawa mataimakinsa, Aliyu Makaman Bidda, cewar ya tsaya a filin jirgi ya taryi Akintola idan ya karaso, domin shi zai wuce Masallaci. Cikin raha da kakaci, sai Makaman Bidda yace masa, ranka ya dade, shin ka maida ni arne kenan ni ba zan je Sallah ba? Firimiya ya mayar masa da amsa, cewar bana nufin haka ko kadan, illa kawai ina nuna maka matsayin ka na mataimaki, a lokacin da bana nan ka tsaya ka wakilce ni. Nan dai Makaman Bidda ya nunawa Firimiya muhimmancin ya tsaya da kansa ya taryi Akintola din, idan ya so yayi Sallar azahar a filin jirgin, nan dai Firimiya ya gamsu, suna cikin yin Sallar Azahar ne sai jirgin su Akintola ya sauka. Bayan su Firimiya sun idar da Sallah ne, aka ĸanyi kade kade da bushe bushe na taryen manyan baki kamar yadda aka saba ana taren baki na alfarma. Daga nan Firimiya ya gabatar da Ministocinsa ga Samuel Akintola, a lokacin da muke kokarin fita daga zauren karbar baki, sai muka hangi Gilmawar Mejo Chukwuma Nzeagwu a cikin kakin soja, sai Firimiya ya tambaya me Nzeogwu yake yi a cikin filin jirgin sama sanye da kaki? Sai Akintola ya tambayi Firimiya ko da matsala ne? Sai Firimiya yace, abun mamaki ne naga Soja da kaki yanzu yana zirga zirga, daga nan su duka biyu sukai dariya suka wuce muka fita dan hawa mota. Na wuce gaba na tuka su, zuwa gidan saukar baki na Gwamnati, inda Firimiya ya shiryawa bakin liyafar cin abincin rana shi da 'yan tawagarsa, sannan kuma su yi tattaunawa a kebe. Akintola ya dan yi min hasafi (inji Direban sardauna) Har ma dogarinsa yake cewa nai masa wani abu shima. A lokacin naji mutane suna fadin cewar, Akintola ya gayawa Sardauna cewar, a yanayin yadda abubuwa suke faruwa, Gara su nemi mafaka a wata kasar su bar Najeriya, amma dai ni banji wannan magana daga bakin su ba, a wajen jama’a naji. Bayan sun gama tattaunawa, bakin sun gama cin abinci, muka dauko su dan raka su filin jirgi, domin komawa. Anan ne, muka sake ganin Mejo Chukwuma Nzeagwu, wannan karon yana sauri yana bin Kwambar motocin mu, kamar akwai wani abu da yake son fadawa shugabannin guda biyu. Bayan da Akintola ya hau jirginsa ya koma, suka yi Sallama da Firimiya. Muka kama hanya dan komawa gidan Gwamnati, sai Firimiya ya lura Nzeogwu yana biye da shi a baya. Da yaga haka, sai yace, maza yi kwana ka kaini cikin gari na dan motsa jik a otal din Hamdala, anan ne galibi Firimiya kan tsaya ya shakata a lokacin da yake hutu baya aikin komai, kafun mu isa wajen, sai Firimiya yace, na kaishi gidan kwamashinan 'yan sanda na lokacin, MD Yusufu, muna isa gidan sai muka tarar Kwamashina baya nan, mun iske wani dan sanda yana gadi a bakin Kofa, dan sandan dake gadi ya tambayi Firimiya, idan ya dawo wa za a ce masa ya zo? Sai Firimiya yace masa, ka gayawa oganka, wani dogon mutum me gashin baki yazo bai same shi ba. Sannan Firimiya ya zaro Fan daya ko biyu a aljihunsa ya baiwa dan sandan. Da muka fito daga gidan MD Yusufu, sai na tambaye shi, ina kuma zamu je? Sai yace na kai shi unguwar Kakuri, muna zuwa Kakuri sai ya shaida min cewar yana son zai kai ziyara DIC (Defence Industry Cooperation), muna gab da isa bakin kofar shiga, sai muka ga an rubuta baro baro, 'No Enter By Order' ma'ana ba wanda zai shiga sai wanda aka yiwa izni. Sai na gayawa Firimiya cikin raha cewar, Mubi fa a hankali sojojin nan zasu iya harbi, ba hankali gare su ba, Firimiya bai ce komai ba, da yake da Azumi a bakinsa, sai na kalle shi ta madubi muka hada ido, sai yace mun, kana zaton ko bacci nake? Sai nace masa, ranka ya dade naga kayi tagumi ko akwai wani abu da yake faruwa ne? Sai yace, kawai ina tunanin wannan rayuwar ne, sai na sake tambayarsa, ko da akwai wata matsala ne? Sai yace mun, bai san me zai faru da shi ba idan ya mutu, sa ya kara da cewar "bana fatan na kara shekaru biyar nan gaba" yace gaskiya shi ya gaji da wannan rayuwar. Sai nace masa, haba ranka ya dade ya zaka dinga irin wannan tunani, ai kullum addu'ar mu Allah ya baka lafiya da yawan rai. Nace masa, Yallabai, idan ka mutu yanzu, akan idon mu komai zai jagwalgwale a kasarnan, sai ya kara cewa, ni dai wannan rayuwa ta ishe ni. Daga nan sai yace, na maida shi gidan Gwamnati. A lokacin biyar na Yamma ta kusa, an kusa Shan Ruwa, muna isa gida har ya bude Kofa zai shiga sai ya kira daya daga cikin hadimansa, Mamman Bakura, ya shaida masa cewar, idan an kira Sallah kusha ruwa Kada ku jirani, shi kansa Bakura yayi mamaki domin mun saba da Firimiya muke buda baki tun farkonsa Azumi. Leadership: ka bayyana mana abubuwa na karshe da suka faru da Sardauna a gaban idonka? Sarkin-Mota: Bayan da aka yi Sallar Asham, sai Firimiya ya sauko daga sama ya shaida mana cewar kowa yana iya tafiya ya kwana cikin iyalansa, sai daya daga cikin hadimansa da ake kira Jarumi, yace shi yana nan ko bukatar gaggawa zata taso. Ni kuma ina tare da a iyalina a gidan Gwamnati a bangare na, da Misalin karfe daya na dare, ina wanke mota a lokacin, sai Firimiya ya sauko yana kwalawa me askinsa kira, yazo da sauri, da yazo sai ya gaya masa yana son yayi masa asiki a daren. Sai ya tambayeni da su wa yaga in magana dazu? Sai nace masa da 'yan sandan da suke gadin gidan Gwamnati muke magana. Ashe ban sani ba, nayi kuskure, mutanan da na zata masu gadi ne, ashe sojoji ne, tuni sun shigo gidan a sace, sun rarraba kansu kusfa kusfa. Daga nan Firimiya ya aiki Bakura ya sayo masa kilishi da balangu, daga nan Firimiya yace na zo, na hau sama na daukowa masu gadin Lemo su sha, na shiga na dauko musu 'Tango'. A wannan lokacin bamu sani ba ashe, tuni wadannan sojojin sun kashe masu gadin gidan Gwamnati, suna gani na, suka kirani suka ce nai maza maza na bar gidan, kafun na tafi sai daya daga cikinsu yace mun 'ina Sardauna yake' Sai na nuna masa ban san wa yake tambaya ba, a lokacin wajen karfe daya da rabi na dare, sai ya sake tambaya ta, ina Sardauna yake, nace musu, tun da yamma da muka dawo daga Hamdala ban mu sake haduwa ba. Su uku ne, sojojin, sai daya daga cikinsu yace, sun bani dakika biyar na fada musu inda Sardauna yake ko su kashe ni. Sai nayi karfin hali, nace musu, kuna iya kashe ni idan kun so, sai suka kyale ni suka shiga cikin gidan suna neman dakin da yake, a lokacin nan sun duba ko ina basu ganshi ba, daga nan suka shiga sashin da iyalansa suke, suka fito da su waje, suna tambayarsu ina Sardauna yake, ana haka, sai iyalan Firimiya suka garzayo inda nake suka hadu da iyalina. Sai kawai muka fara jin sojojin suna harbi ratata, na kirga harbi yakai sau goma, daga nan suka budewa dakina wuta a zaton su Firimiya yana ciki, suka karya Kofa suka shiga, suka farfasa gilasai, suka birkita dakin amma basu ga Firimiya ba. Daga nan sojojin suka shiga harbin kan mai uwa da wabi, anan ne fa, iyalin Firimiya suka shiga kururuwa, Inno matarsa, tana ta cewa, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, daga nan, sai daya matar tasa Hafsatu ta hango Firimiya sanye da doguwar Jallabiya kansa babu hula yana tsaye, sai tayi sauri ta mika masa mayafinta, ta ce ya lulluba yayi basaja ya gudu. Sai Firimiya yace mata, ba zai saka ba, ai shi suke nema kuma gashi. Nima na tashi da sauri na karasa inda Firimiya yake, na kamo hannunsa, amma ina ya dage. A lokacin nufi na shi ne, na kamo shi, na jashi zuwa dakina na b'oye shi, tunda sun tabbatar baya ciki, amma ina da wani yayo harbi sai na wuntsula na bar Firimiya a tsaye. A lokacin sojojin suka kashe wutar gidan gaba daya, sai Inno ta taso a guje dan ta zo inda Firimiya yake, ashe wani soja ya hango ta, kawai sai ya biyo ta a baya, yana fadin, Ina Sardauna yake, jin haka sai Firimiya yayi magana yace gani nan, Allahu akbar! Anan wajen Ajalinsa ya sauka, Firimiya yana tsaye kusa da wani makewayi, matarsa Hafsatu ta rukunkumeshi, sojan kuwa, fadi yake ta sake shi ko ya bude musu wuta gaba daya, amma ina Ajali yayi kira, bata ko saurare shi ba. Ta gayawa sojan ka kashe ni tare da shi, daga na kuwa bai yi wata wata ba ya bude musu wuta su biyun, akan idona, Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto aka kashe shi tare da matarsa Hafsatu a lokacin. Karfe 4 na asubahi tayi, na suma da ganin gawar Firimiya tare da matarsa a gabana. Kun ji yadda sojoji suka kashe Sir Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto Firimiyan Jihar Arewa a Kaduna ranar 15 ga watan Janairun 1966. Allah ya jikansa yaji gafarta masa...Ameeen Ya Allah!!!

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15