Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya daga birnin Landan inda ya je bayan taron majalisar Dinkin Duniya na 2017. Shugaban kasar ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe a yammacin ranar Litinin, 25 ga watan Satumba bayan kwanaki hudu a birnin Landan.
A ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga birnin New York zuwa Landan kamar yadda Femi Adesina ya sanar.
Shugaban kasar ya biya Landan a hanyarsa ta dawowa Najeriya. Amma dai fadar shugaban kasar bata bayyana ko tafiyar Buharin na da alaka da lafiya ba.
Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya ce ba zai iya tabbatarwa ba idan shugaban kasar zai je ganin likitocin sa ne a Landan.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15