Hukumar tace fina-finai ta musanta janye dakatar da Rahama Sadau
Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, KSCB, ta musanta jita-jita dake yawo a gari cewar ta umarci kungiyar masu shirya fina-finai ta MOPPAN data mayar da Rahama Sadau bakin aiki. Daraktan hukumar tace fina-finai ta Kano, Isma'il Na'abba Abdallah, ya bayyana hakan a wata ganawa da kamfanin jaridar Daily Trust ta waya.
Jita-jitar mayar da Rahama Sadau din dai ba zata rasa alaka da wani hoto da Sadau din tayi da shugaban hukumar tace fina-finan tare da shahararren jarumin wasan Hausa, Ali Nuhu, Sannan da fitowar data yi kafafen yada labarai a jihar Kano ta bayar da hakuri ga Gwamnan jihar da kuma sarkin Kano bisa fitowar ta cikin wani faifan bidiyon waka da bai yiwa jama'ar Kano dadi ba.
Sannan ya kara da cewa " Zamu goyi bayan duk matakin da kungiyar MOPPAN ta dauka a kan Rahama Sadau, amma maganar gaskiya bamu umarci a dawo da ita ba, illa iyaka idan kungiyar da kanta tayi na'am da nadamar data yi kamar yadda ta aike mana gabadaya a rubuce, ta dawo da ita, mu bamu da haufi a kan hakan, saidai ba zamu yi wani yunkuri na ganin kungiyar ta janye matakin data dauka a kanta ba " Kungiyar MOPPAN ta kori Rahama Sadau daga kamfanin shirya fina-finai na Kannywood ranar 3 ga watan Oktobar 2016 bayan data fito cikin faifan bidiyon wata waka da kungiyar tace ya sabawa dokokinsu na sana'ar wasan kwaikwayon Hausa.
Comments
Post a Comment