Kwanan nan zan yi sabbin nade-nade – Buhari



Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce nan ba da jimawa ba zai yi sabbin nade-nade a gwamnatinsa domin amfanar jama'ar kasar.
Shugaban kasar ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a taron koli na jam'iyyar APC mai mulki da aka gudanar ranar Talata a Abuja.
Ya ce "za a fadada Majalisar zartarwa ta hanyar nadin magoya baya da za su kawo sabbin dabaru kan yadda ake tafiyar da gwamnati." Shugaba Buhari ya kuma bayyana takaicinsa kan jinkirin da aka samu wajen nadin mambobin kwamitocin gudanarwa na hukumomin gwamnatin tarayya.
Ya danganta jinkirin ga wasu kwamitoci daya kafa don tabbatar da cewa an zabo mutane daga kowane bangare na kasar a kwamitocin gudanarwa na hukumomin gwamnatin.
" Ya ce na san cewa magoya bayan mu sun kosa su ga an yi nade-naden, amma nan ba da jimawa ba za'a sanar musamman ganin yadda tattalin arzikin kasar ya inganta''.
Tun bayan daya dawo jinya daga Birtaniya a watan Agusta ne ake ta kiraye-kirayen shugaban ya sauke wasu daga cikin ministocinsa. Sai dai Shugaba Buhari bai yi karin bayani ba a taron koli na jam'iyyar APC akan ko zai sauke wasu ministocinsa.
Masu lura da al'amaru dai na ganin babu kyakkawar dangantaka tsakanin shugaban kasar da wasu ministocinsa, musamman yadda wasu ministocin ba sa iya ganin shugaban kasar a duk lokacin da suke so.
A kwanakin baya ne aka tseguntawa manema labarai wata wasika da ministan mai Dokta Ibe Kachikwu ya aikewa shugaban kasar.
A cikin wasikar dai ministan ya nuna damuwa kan kokarinsa na ganawa da shugaban kasar a lokuta daban-daban amma bai samu dama ba.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15