Abin da ya kai mu wajen Buhari – Sheikh Bala Lau



Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatul Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya shaida wa BBC dalilin da ya kai su fadar shugaban Najeriya.
A farkon watan nan ne wadansu malaman addinin Musulunci a kasar suka kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.
Sheikh Bala Lau ya ce dalilin zuwansu fadar bai wuce batun cewa shugaban ya kwashe lokaci mai tsawo bai sadu da malaman addinin ba, tun gabanin ya fara jinya a farkon shekarar nan. Malamin ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan ranar Alhamis tare da rakiyar Sheikh Kabiru Gombe.
"Ba kawai malunma na addinin Musulunci shugaban ya gani ba. A'a har da ma malaman addinin Kirista ya gana da su a lokacin," in ji shi.
Ya ci gaba da cewa: "Babu shakka mun shaida masa halin da talakawa suke ciki har ayoyin Al'kur'ani sai da na karanta masa."
Har ila yau malamin ya ce sun bukaci shugaban da ya rika kawo sauki a cikin shugabancinsa. Kuma ya ce shugaban ya ba su tabbacin aiki da shawarwarin da suka ba shi.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15