Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa aure na ya mutu - Jaruma Asma'u Sani



Fitacciyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood Hajiya Asma'u Sani ta fito tayi karin haske game da ainihin musabbabin dalin mutuwar auren ta a kwanan baya bayan ta shafe shekaru a gidan mijin nata.
Hajiya Asma'u da tayi tsokaci game da hakan a yayin wata fira da tayi da majiyar mu ta bayyana cewa mijin ta da aura a shekarun bayan ya yi zato ita wata hamshakiyar mai kudi ce musamman ma saboda yadda yaga tana fitowa amatsayin mace mai kudi a cikin fina-finan ta da dama.
Majiyarmu dai ta samu cewa sai dai a tun lokacin da ya gano ba haka lamarin yake ba, a cewar ta sai ya fara wulakanta ta yana ci mata mutunci daga baya kuma har yazo ya sake ta.
Daga nan ne ma kuma sai jarumar ta yi kira ga sauran al'ummar dake yi mata kallon kamar taki son zaman aure ne da su yi mata uzuri don kuwa ta matukar son aure don a cewar ta ko gobe idan ta samu miji zata sake yin aure domin shine suturan dukkan 'ya mace.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15