Dandalin Kannywood: Jarumi Ali Nuhu ya lashe wata muhimmiyar kyautar karramawa



Fitaccen jarumin nan na wasan fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood kuma jigo Ali Nuhu zai karbi wata kyautar karramawa ta musamman a wajen bukin karrama yan wasan fina-finai a Najeriya na wannan shekarar da aka yi wa lakani da 2017 Best of Nollywood Awards.
Kamar yadda muka samu dai daga shugaban kamfanin da ke bayar da award din, Seun Oloketuyi ya bayyana cewa fitaccen jarumin Ali Nuhu ya cancanci kyautar duba da yadda ya dade yana bada gudummuwar sa shekara da shekaru a masana'antar.
Majiyarmu dai ta samu haka ma dai daga majiyar tamu cewar za'a gudanar da bukin karramawar a ranar 16 ga watan Disemba mai kamawa a dakin taro na al'adu a garin Abeokuta, jihar Ogun. Haka ma dai dai Mista Seun din ya kara da cewa Ali Nuhu yanzu ya riga ya zama bangon jingina a masana'antar fim ba ma a kasar Hausa ba kadai amma har da kasar baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15