Dandalin Kannywood: Na fuskanci kalubale wajen shirya Fim akan masu garkuwa da mutane – Zaharaddeen Sani
Fitaccen jarumin Kannywood, Zaharaddeen Sani ya fitar da wani sabon Fim mai suna ‘Abu Hassan’, wanda ya shirya shi da nufin fadakar da jama’a akan aikin masu garkuwa da mutane.
Daily Trust ta ruwaito Zaharaddeen yana fadin bai taba yin Fim kamar Abu Hassan ba, inda yace, labarin shi ne, kuma shi ya kirkiro basirar Fim din, inda yace sabon salon satar mutane daya addabi kasar nan ne ya tunzura shi shirya Fim din, tare da nuna jarumtar Yansanda da Sojoji wajen kare rayukan mutane.
Gogan naku ya bayyana cewa sakon dayake da nufin isarwa shine a daina sauraron miyagu mutane masu garkuwa, inda yace hukunci daya dace da su shine a yi musu kisan gilla.
Majiyar Hausazone.com ta ruwaito Zaharaddeen yana gode ma Adam A Zango daya fito cikin fim din, tare da irin goyon bayan daya ba shi a yayin shirin, tare da Daraktan Fim, Mohammed Alfa Zazi.
Sai dai yace bababn kalubalen daya fuskanta itace wajen tantancewa Fim din, inda suka nuna rashin amincewarsu da sunan Fim din, Abu Hassan, sai dai yace daga bisani sun gamsu da sunan, bayan ya shaida musu cewa ya samo shi ne cikin wasu fina finan indiya daya kalla.
Daga karshe Zaharadden ya yaba ma hukumar Sojoji, wanda yace sun taimaka masa da kayan Sojoji da bindigun da yayi amfani dasu a cikin Fim din.
Comments
Post a Comment