Zancen Iska Ne A Ce An Cire Ni Daga Shugabancin PDP Ta Jihar Kano –Dan Sharu
Bayan tasowar wata takadamma a jam’iyyar PDP ta Jihar Kano, wakilinmu ya samu zantawa da Alhaji Rabiu Dansharu, wanda ake rade-radin cewa an cire shi daga cikin shugabannin jam’iyyar ta Jihar Kano.
Wakilinmu ya tambayi sharu, “wasu na bada sanarwar cewa sun cire ka daga shugabancin PDP na jihar Kano da kake jagoranta,wane mataki ka ke kai yanzu.” Dan sharu ya amsa da cewa, “Kamar yadda ka sani da al’umma ma suka sani. Ita jam’iyya wani abune wanda yake “institution” na kanta kuma tanada tsarin mulki irin yadda kasar nan ke da tsarin mulki.
Tsarin mulkin PDP shi ya kawo ni, kuma shi ne za ka iya bi ka bada irin wannan labari, irin wanda suka fada, amma tunda an ce sun zare ni daga shugabancin jam’iyya. To na san ba wasu mutanene suka sani shugabancin jam’iyya ba,al’umma ne yan jam’iyyar PDP sukazo suka jefa min kuria na zabe aka zabe ni har na zama shugaba,kuma idan akwai tsari wani yanada tunanin za,a zareni a ciki to da tsarin aka bi to ba a kano zaka jishi ba,domin a matsayina na shugaban jam’iyyar PDP Jihar Kano. Ni mamba ne na kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP na kasa duk taronda za,ayi dani za,ayi.kuma tsarin mulkin jam’iyya shafi na 98 inka dubashi zakaga an fadi cewa babu wani ko wasu a jiha da suka isa u tuhumi shugaban jam’iyya na jiha akan kowane irin tunani illa shugabannin jam’iyya na kasa.Wanda shi ake cewa”NEC”Sune sukeda ikon suyi wannan,to in ance wasu mutane sunce sun tsigeni a kano kaga iskace kawai ba wani abu ba.
“Duk dai maganar kwara dayace kamar yadda na gaya maka bazaka dora akan abin da bashida hujja ba abin da bashida hujja kuma ba,a yishi akan tsari ba,ka tsaya kana bada amsa akanshi kuma aika yarda dashi kenan.
Wannan labari ne na kawai wanda kowa yaga dama yana iya zuwa ya fadi abin da dama,duk wanda aka fadawa shi kuma ya rage ga mai hankali ya duba yaga menene gaskiyar magana meye karyar magana a ciki,a yanzu maganarda muke ba wani amsa dazan iya baka kan wannan domin ba a doron yadda yakamata ace anyi aka yiba,koda mutane sunyi wani abin ba,bisa tsarin ka,ida ba ace in basu amsa to ai kaga na zama daidai dasu kenan.
“To ai siyasa sha,awa ce kowa yanada nasa ba zan iya fitowa ince maka ai daga wajen wane ya taso ba amma da alama daga yadda mukaji,yadda aka yi al,amarin ance a gidan wani aka yi,kuma shi ya kasa ya tsare domin su tabbata anyi suka kaa suka tsare ta yiwu daga wajensu ya taso ban sani ba.
“Tabbas wannan magana magana taka zan yarda da ita,zai iya zama nakasu,amma watakila su mutanen nan da ake magana dama kwangila aka basu dansu kawo nakasu shi yasa sukeyi,amma tunda shugabanci na hannunmu muna bincike mu gano su waye sukeda hannu a cikin wannan domin ayi hukunci da tsarin mulki ya tanada,abin da nake tabbatarwa da yan jam’iyya wannan duk zance ne mara tushe na iska kar hankalinsu ya tashi.Kuma sai mu yiwa Allah godiya yan jam’iyyane suka yi wannan to wannan alama ce ta bunkasar jam’iyya,akwai wadanda basa fahimta da wadanda aka tilastasu su shiga ciki,akwai wadanda su kuma yan su bata ne,wannan kashi 3 kashi daya ne kadai zaka yaka,wanda bai fahimta ba ka fahimtar dashi,wanda aka tursasa ka yi masa furuci dazai fahimta shima a ganar dashi,amma idan mutum zaiyi dan ya nakasa jam’iyya saika yakeshi shi kuma.” Inji shi Lokacin da wakilinmu ya tambaye shi dangane da shugabancin jam’iyyar ta PDP kuwa, ko shin har yanzun shi ne shugaba, sai Sharu ya ce, “Ana da ja ne? Yau idan naje na ce kai ba kana cikin wakilan wannan jarida bane,shi kenan ta tabbata? Bani na saka ba akwai tsari da za,abi,ko masu gidanka sai sunbi tsari yadda ake sauke ma’aikaci. Zanen ma kace wannan na nuna nine shugaban jam’iyya ina zaton dan nine shugaban kazo wajena.
Wane kira kake dashi ga yan jam’iyyarku anan kano gameda wannan matsala. Munyi kiraye-kiraye anyi bayanai,wannan al,amari su watsar dashi ba magana bace ta gaskiya,ba wata rigima a PDP kowa ya kwantarda hankalinsa,so ake a nuna akwai rigima da fitina,bamuda ita in Allah ya yarda kuma wannan tsari zamu zauna a kawo gyara yadda za,a fahimci juna a dora domin mu sami nasara.”
Comments
Post a Comment