AN JEFAR DA JARIRIYA DAUKE DA TAKARDAR WASIYYA A BIRNIN KEBBI
Daga Hamza Ahmed
Hukumar Hisbah ta jihar Kebbi ta gabatar da wata jaririya da aka haifa aka jefar a unguwar shiyar Sarakuna kusa da makarantar 'yan Mata mai suna Unity College a ranar Juma'a 22/12/17 da misalin karfe 11:00 na dare.
Yariyar an tsince ta ne cikin hijab, inda mahaifiyar yarinyar ta rubuta wasikar wasiya ta bari tare da jaririyar.
A cikin wasikar ta roka da don Allah a kula mata da diyarta ta, jefar da ita ne a dalilin tsangwamar da mahaifiyarta ta yi mata na a kashe jaririyar, shine ta zabi ta jefar da ita.
Ta kara da cewa tana rokon a sakawa jaririyar tata suna Aisha don shine sunan mahaifiyarta, ta kuma yi alkawarin cewa komai dadewa za ta waiwayo 'yartata.
Alh Abubakar Muhammad Lanne Augie, wanda shine Daraktan Shari'a a hukumar Hisbah, ya yi bayanin cewa wanna shine karo na farko da suka taba ganin irin wannan na a jefar da diya da wasiyya.
Ya yi bayanin cewa rokon da mahaifiyar yarinyar ta yi na a sawa diyar tata sunan mahaifiyarta, ya ce sun cika alkawarin, inda suka anso mata 'Court affidavit' dauke da sunan da ta roka a sawa diyar.
Daraktan ya kuma yi Allah wadai da yadda yawan jefar da yara ke karuwa.
A nasa bangaren, shugaban hukumar hisbah ta jihar, Alhaji Suleiman Muhammad ya yi kira ga musulmi su kara hada kai don sa ido a ga cewar an kawo karshen wannan lamarin. Ya roki Allah da ya shiryar da wannan matar ya kuma yi addu'a Allah ya raya wanna jariryar.
Domin karin bayani a tuntubi wanna lambar 07064343965
Comments
Post a Comment