An yiwa shahararrun mawakan Najeriya biyu sata a cikin jirgin sama
Fitattun mawakan Najeriya biyu sun gamu da sharrin 'barayi
- An yi masu satar ne a cikin jirgin su a filin tashi da saukar jirage na jihar Legas
- Wani na kusa da mawakan ya tabbatar da faruwar al'amarin
Wani jirgin sama na musamman dauke da fitattun mawakan Najeriya, Wizkid da Tiwa Savage, ya gamu da sharrin barayi yayin da yake gare kafin ya gama tsayawea a filin jirage na Murtala Muhammed dake Legas.
An yiwa mawakan satar ne bayan dawowar su daga Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom. Jirgin mai lamba T7-Aoo ya sauka a filin jiragen na Legas da misalin karfe 8:33 na yamma kuma an yi masa sata yayin da yake gare kafin ya kai ga tsayawa.
Jirgin ya tsaya domin wani jirgin kaya yana gabansa. Bayan jirgin ya tsaya ne, direban mawakan ya kula da cewar an balle kofar sashen ajiyar kayan fasinja na jirginsu kuma nan take ya sanar da jami'an filin tashin jirgin, amma kafin su kai ga inda ake zargin an yiwa jirgin fashi, barayin sun gudu.
Jakankunan da aka dauke a cikin jirgin mallakar Wizkid ne da Tiwa Savage.
Jaridar Sahara, wacce ta wallafa labarin, ta ce ko a ranar 16 ga watan Disamba saida aka yiwa wani jirgi sata bayan saukar sa a Legas daga kasar Turkiyya.
Jaridar Sahara Reporters ta ce wani makusanci ga mawaki Wizkid ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin da Tiwa Savage ta bayyana fushinta da faruwar lamarin a dandalin sada zumunta.
Comments
Post a Comment