An Kama Matashi Ya Sha Maganin Kara Karfin Jima'i Ya Yiwa 'Yar Shekaru 14 Fyade



Jami’an ‘yan sanda a jihar Kaduna sun kama wani matsashi mai shekaru 32 da haihuwa da ake zargi da yiwa yarinya mai shekaru 14 da haihuwa fyade har ya kusa hallaka ta.
A jiya laraba ne mai magana da yawun jami’an ‘yan sandan jihar Kaduna ASP Aliyu Usman ya yiwa manema labarai bayanin cewa matashin mai suna Hamza Abdullahi, wanda ke zama a Unguwar Rigasa, yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna ya shigar da yarinyar mai shekaru 14 da haihuwa dakinsa wanda yake kusa da gidan iyayen ta kuma ya yi jima’I da ita.
Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya sha maganin karawa maza karfin jima’I kafin lamarin ya auku inda ya yi ta jima’I da ita har sai da ta fita daga haiyacinta.
Mujallar Daily Post, ta bayyana cewa yayin da ya lura cewa, karamar yarinyar bata numfashi, cikin gaugawa ya nemi taimakon mai Keke Napep domin ya taya shi daukar gangar jikin zuwa wani daji dake kusa da unguwar inda yayi niyar jefar da gangar jikin, amma cikin rashin sa’a sai wani daga cikin ‘yan uwanta ta gansu a lokacin da suke kokarin dora ta akan keke Napep.
Da ganin haka ne sai ta daga murya lamarin da ya ja hankalin jama’a masu wucewa, wadanda ganin yanayin da yarinyar ke ciki yasa suka hau matashin da duka, amma jami’an ‘yan sandan unguwar Rigasa suka kwace shi inda suka garzaya da shi ofishin su.
Da yake Magana da manema labarai a ofishin jami’an ‘yan sandan jihar, Hamza ya amsa cewa ya yi jima’I da matashiyar mai suna Fa’iza Salisu amma a cewar shi yayi haka ne tare da yardarta domin ya yi mata alkawarin zai bata kudi.
Hamza wanda ya karyata zargin sa da shan maganin Karin karfin jima’I ya bayyana cewa ya sha wani magani da wasu mata ke sayarwa a unguwar.
Mai Magana da yawun jami’an ‘yan sandan ya bayyana cewa suna ci gaba da bincike kan lamarin, ya kuma kara da cewa zasu tura matashin kotu da zarar sun kammala bincike.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15