Dandalin Kannywood: Tsohuwar jaruma Abida Muhammad ta sake aure na 2



Tsohuwar jaruma Abida Muhammad ta sake aure na 2
- Jrumar ta sake aure ne a ranar 26 ga watan Janairun shekarar nan da muke ciki
- Jrumar ta auri masoyin ta ne mai suna Al-Mustapha Abubakar akan sadaki Naira dubu 100 Labarin da muke samu sun tabbatar mana da cewa tsohuwar fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta sake zama amarya a karo na biyu a rayuwar ta.
Mun samu dai cewa jarumar ta sake aure ne a ranar 26 ga watan Janairun shekarar nan da muke ciki biyo bayan rasuwar mijin ta da suka kasance a tare na tsawon shekaru mai suna Marigayi Hamza Danzaki.
Hausazone.com haka zalika ta samu cewa jarumar ta auri masoyin ta ne mai suna Al-Mustapha Abubakar akan sadaki Naira dubu 100 da aka biya nan take da kuma aka gudanar a garin Kano.
Fitacciyar jarumar dai ta yi tashe sosai a masana'antar shirya fina-finan na Hausa a shekarun baya inda ake kallon ta a matsayin daya daga cikin fitattun jaruman da suke da kwarewa musamman ma wajen rawa.

Comments

Popular posts from this blog

BRIEF BIOGRAPHY OF SHEIKH IBRAHIM AHMAD MAQARY, IMAM OF NATIONAL MOSQUE ABUJA

Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Karanta cikakken tarihin sa

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.