Matata Zindir take yi tana tsine min idan rikici ya hada mu – Magidanci



Wani limamin coci mai suna Bernard Towoju ya roki kotu dake Igando a jihar Legas da ta warware auren sa da matar sa Abosede saboda yadda zindir da take yi tana tsine masa da gabanta a duk lokacin da suka yi fada. Bernard wanda ke da shekaru 53 ya ce matar sa mafadaciya ce sannan tana da taurin kai wanda hakan ya sa ba zai iya ci gaba da zaman aure da ita ba.
” Saboda yawan fadan da muke yi kullum dole na tattara nawa inawa na bar mata gidan da na gina shekaru 10 da suka wuce na koma zaman gidan haya amma duk da haka ban kubuta daga masifar ta ba. Harta ofishin ‘yan sandan dake unguwar mu da makwabta sun saba jin mu.”
Ita Abosede mai shekara 46 wanda ke sana’ar Tela ta na zargin mijinta da yin watsi da ita da ‘ya’yan su hudu har na tsawon shekaru 10. Duk da cewa Abosede ta roki kotu kada ta warware auren, daka karshe dai Alkalin kotun Akin Akinniyi ya raba auren.

Comments

Popular posts from this blog

BRIEF BIOGRAPHY OF SHEIKH IBRAHIM AHMAD MAQARY, IMAM OF NATIONAL MOSQUE ABUJA

Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Karanta cikakken tarihin sa

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.