Mu Dage Don ‘Yan Kudu Su Yi Koyi Da Mu- BOC
Daya daga cikina matasan da suke wakokin Ingausa (Hip-Hop) Smartkid, Skd yana kara bai wa ‘yan uwansa mawakan Arewa kwarin guiwa kan cewa su ma su dage muma ‘yan kudu su yi koyi da mu, ta hanyar kawo sabbin abubuwa a fannin Hip-Hop na harshen Hausa, ya kuma ce ba lallai ne mu rika daukar wakar su muna juya wa ba, muma za mu iya kirkirar ta mu, kuma ta karbu a duniya fiye da ta su,.
Hadin kai kadai muke bukata, abin da nake nufi da hakan shi ne, muma manyan da suka iya kuma suka karbu a idon duniya mu dage mu daga na kasa da mu don su nuna wa duniya irin baiwar da Allah Ya yi wa Arewa baki daya.
Ya kuma kara da cewa idan muka duba rayuwar mawakan Hip-Hop na kudu, kullum burinsu su ga sun daga junansu, daga sanda suka ga tauraruwarsu ta fara disashewa, sai su fara zakulo na kasa da su ‘yan kudu suna haska su. Misalin in kuka duba rayuwar Don jazzy, ganin cewar ya fara sanyi, sai ya kirkiri kungiyar Mabin Record, wadda ya sanya kananan mawaka masu tasowa kamar su, Reekado Bank, Koredo Bello, Dija, Tiwa Sabage, da dai sauransu.
Haka shi ma Olamide, Ganin tauraruwarsa tana haskawa yana wakoki suna karbuwa sosai a idon Duniya, sai ya kirkiri kungiyar YBNL don ya taimaka wa na kasa da su, kuma ‘yan kabilarshi, Kungiyar da ta hada yara kamar su, Lil kesh, Adekunle Gold, bictor, Sikibi da dai Sauransu. Ya rika basu wakoki da suka haskaka su.
Sannan in kuka duba irinsu, Ice Prince ‘yan Arewa ne da suka shiga kudu, sai suka kirkiri kungiyar Chocolate City wadda a cikinta ya hada da manyan mawakan Arewa, kamarsu jassy jags, AKA Kila, da sauransu.
Wannan kungiya ta yi rawar gani wajen haska tauraruwar ‘yan Arewa sosai.
Muma a nan Arewa za mu iya yin hakan, kuma zai taimaka mana kwarai da gaske, ta hanyar kirkirar kungiyoyi ko saka kananan mawaka a cikin wakokin mu, mu taimaka wa juna da mu sake fito da sunan Arewa kamar yadda su ma suke taimakon bangarensu.
Sannan mu yi kokari mu kauce wa kalaman Batsa a cikin wakokinmu, da kuma ha’intar juna ko ganin nafi wancan ba zan taimaka mashi ba, mu zama tsintsiya ma daurinki daya hakan zai taimaka mana kwarai kuma Arewa za ta zama abin koyi.
Ina So Na Zama Gwani A Duniya –DSB Shaharerran mawakin Ingausa (Hiphop) Nuradden wanda aka fi sani da Deeni star boy wanda ya rera wakar SHIGA DA KAI, ya kuma yi ZUWANTA NE da wakar DAB a harshen Hausa. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu Muhsin, ya yi muhimman bayanai dangane da harkarsa ta waka, ga yadda hirar ta kasance:
Comments
Post a Comment