SHARHIN FINAFINAI: Sharhin Fim Din ‘Diyya’3





Daga Saddika Habib Abba
Suna: Diyya
Tsara labari: Munzali M Bichi
Furodusa: Naziru Auwal Dan hajiya
Bada umarni: Ali gumzak Sak
Kamfani: Smart Studio
Jarumai: Ali Nuhu, Aminu Sheriff, Fati Washa, Rabi’u Rikadawa, Shehu Hassan Kano, Ladidi Fagge, Hadiza Muh’d, da Mustapha Musty.
A farkon fim din an nuna Natakari (Rabi’u Rikadawa) wani Alhaji yazo akan zai koreshi daga gidan haya saboda bai biya kudin haya ba dakyar Natakari ya lallabashi suka tsaida magana akan sati biyu masu zuwa zai ba shi kudinsa idan kuma ba haka ba zai kore shi Natakari yaji dadin wannan alfarma da aka yi masa amma duk da haka a lokacin ya fara tunanin a ina zai sami kudin hayar a wannan karamin lokacin domin ba shida dalilinsu.
A na cikin haka sai matarsa Murja(Ladidi Fagge) ta aiki ‘yarsu Maimuna siyan kosai da safe Maimuna ta zo fita a soron gidansu sai ta ci karo da gawa an lullubeta ta fice daga gidan da gudu a gigice tana fita Usman (Isa Feruskan) ya buge ta a mota kuma ya gudu.
Usman dan gidan wani babban mai kudi ne( Shehu Hassan Kano) bayan an shigo da Maimuna gida mutanan unguwa da mahaifan Maimuna kowa ya yi zaton ta mutu sai daga baya iyayenta suka ga ashe suma ta yi, farfadowar data yi cikin kidima Maimuna ta nuna wa iyayenta gawar data gani suna dubawa sai suka ga Saima (Fati Washa) suka kidime domin basu santa ba kuma basu san waye ya ajiyeta ba hakan tasa Natakari ya bullo da hikima domin dama talauci ya ishe shi a kan ‘yarsa Maimuna tunda kowa ya yarda cewar ta mutu.
To, ta gudu kauye shi kuma sai ya je gidansu Usman ya ce an kashe masa ‘yarsa zai yi amfani da gawar Saima saboda haka sai an bashi diyya matarsa ta yi kokarin nuna masa wannan abinda zaiyi ba dai dai ba ne, amma ya ki amincewa ya tafi gidansu Usman ya tsaya kai da fata ya ce dansu ya kashe ma sa ‘ya.
Saboda haka sai an bashi diyya mahaifin Usman ya amince cewar zai biya diyya, amma a kirawo ‘yan sanda da likita su yi bincike, domin a saka hannu Natakari da Alhaji su ka rankaya gabakidayansu su ka tafi gidan Natakari. A na zuwa likita ya bude fuskar gawar domin ya gudanarda bincikensa sai Alhaji ya ga ashe ma ‘yarsa ce ta cikinsa wadda ya ke nema wadda ta bar gida sanadin zai yi mata auren dole.
Ita kuma akwai saurayinta wanda ta ke so, a ta ke labari ya sha bamban Alhaji ya yi umarni da ‘yansanda su tafi da Natakari domin shine ya kashe masa ‘ya Natakari ya rikice ya fara nadamar abinda ya yi aka tafi dashi ana zarginsa da hukuncin kisa abun har yaje kotu bincike tasa har lauyan Alhaji Habib (Ali Nuhu) ya je ya taho da saurayin Saima, wato Kamalu (Aminu Sharif Momo) kuma a ka yi arashi a lokacin da lauyan ya je dakin Kamalu ya tarar da kayan Saima a dakin Kamalu.
Wannan hujjar ce ta saka alkali ya kuma tabbatar da zarginsa a kan Kamalu kuma ya yi umarni a kan ya fada ma sa gaskiya Kamalu ya bawa kotu labarin cewa Saima ta zo ne dakinsa a kan su gudu shi kuma ya ki amincewa kafin ya fita waje ya kawo mata abin sha ya dawo ya tarar har ta mutu.

Shi kuma ya dauketa ya kawo ta soron gidan Natakari. Kamalu ya fadawa kotu shi kadai ne abunda ya sani game da mutuwar Saima a lokacin ana cikin haka likita ya kawo wa kotu shaidar dalilin mutuwar Saima likita ya shaida musu zuciyarta ce ta buga amma babu wanda ya kashe ta a take kotu ta wanke Natakari da Kamalu kuma ta ja hankali akan iyaye masu dagewa sai sunyi yi wa ‘ya’yansu auren dole kuma ya nuna musu illar hakan.
Abubuwan Birgewa:

1- An yi amfani da kayan aiki masu kyau musamman camera ta daukar hoto da sitturu da gidaje wanda suka dace da labarin

2- Jaruman sun yi kokari sosai gurin isar da sakon

3- Zaren labarin ya tafi kai tsaye bai karye ba har ya dire.

4- Shirin ya nuna illar wasu matsaloli da suke faruwa a wannan zamanin na yanzu matsalar auren dole da kuma illar rashin gaskiya da cuta
Kurakurai:

1- Akwai wurin da dan sanda mai kula case din mutuwar Saima yazo ya sami Jamil a hotan an sami matsalar daukewar sauti har aka gama hotan ba’aji mai suke cewa ba.

2- Akwai gurinda Natakari yazo yana yiwa Alhaji masifar an kashe masa ‘yarsa saboda haka sai an biyashi diyya wannan masifar da Natakari yake yi a da yanayinsa a lokacin a gaske hakan bazata faruba shi da aka kashewa ‘ya budurwa duk ina alhinin mutuwar? ai kamar ma yana nunawa Alajin cewar bashida gaskiya ne.

3- Natakari ba shida makwabta ne ko daya ko abokan arziki? acikin unguwa a ture yarinya budurwa ta mutu amma ace babu wanda ya leko gidan jajantawa sai su kadai suke abinsu har asirinsu ya tonu.

4- Acikin kotu yakamata ace dukkan lauyoyi daga dukkan bangarori an gansu kuma sun gabatarda kansu amma mai kallo Barr.Habib kawai ya gani ya gabarta da kansa ba’aga lauyan wanda ake kara ba.

5- An samu matsalar cigaban shiri a kotu a inda ake nuno Murja a zaune da mayafi idan aka kuma nunota kuma sai a ga babu mayafin.

6- Akwa wurinda Fatima take futowa harabar gidanta zata kawowa mai gidanta sako ajikinta babu mayafi ga maigadi ga Natakari a matsayinta na matar aure hakan ya sabawa addini da al’ada.

7- Masu kallo an ga an kulle Natakari a policetation kayan jikinsa an gani duk sunyi datti sun fita a hayyacinsu amma da’aka shigo kotu sai aka ga Natakari da kaya masu kyau harda hula shin Natakari gida ya koma ya canja? idan kawo masa akayi ba’aga sanda aka kawo ba sannan wanda ma yake kulle mai ya hadashi da hula?

8- Akwai wurinda Usman yake ture Maimuna a mota faduwar da Maimuna ta yi male male ga maza sun kewayeta ana hango jikinta hakan ya sabawa addinin musulunci domin ba muharramanta ba ne.

Karkarewa:

Fim din ya yi kyau kuma akwai darussa masu alfanu a ciki, amma wasu abubuwan da a ka nuna faruwarsu zai yi wuya a gaske. Tunda fim din a na kwafo shi daga rayuwar gaske ya kamata a dinga yin abubuwan da kowa idan ya gani zai yarda. Wallahu a’alamu.


Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15