ASABE Madaki, jarumar fim din ‘There is a Way’ da kuma sabon fim din ‘Sarauniya’, ta bada shawarar cewa ya kamata mu yi finafinai da Turanci don mu bada labarin al’adar mu da kan mu. Haka kuma ta fadi yadda a matsayin ta na lauya ta maida hankalin ta ga fitowa a finafinai.
Asabe kwararriyar lauya ce wadda ta ke da matsayin digiri na biyu kuma a yanzu ta na koyarwa ne a bangaren karatun aikin lauya din. Sai dai duk da matakin da ta kai na karatu da aiki a halin yanzu ta samu kan ta a cikin harkar fim, har ma ta fita a finafinai masu dama a Kannywood. Kwanan baya, wakilin mu ya hadu da Asabe a wajen daukar wani fim na Turanci mai suna ‘This is the Way’. Fim din ya na cikin jerin finafinai na Turanci da Kabiru Musa Jammaje ya ke shiryawa.
A hirar su da wakilin mu, Asabe Madaki ta fada masa cewa ita dai haifaffiyar Jihar Kaduna ce, kuma ’yar asalin Karamar Hukumar Jema’a. Ta yi karatun firamare a Command Children’s School da ke Kaduna, sannan a shekarar 2000 ta kammala karatun sakandare a Kwalejin ’Yanmata ta Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke Gusau.
Asabe ta yi karatun digiri a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya daga shekarar 2002-2007 inda ta karanta aikin Shari’a (Law). Daga nan ta yi makarantar koyon aikin Shari’a, wato Law School, da ke Abuja. Sannan ta yi hidimar kasa a nan Abuja.
Don zurfafa ilimin ta, sai jarumar ta yi karatun digiri na biyu a kwas din aikin lauya a kasar Scotland.
“Bayan na dawo kuma ina yin lakca ta rabin lokaci, kuma a yanzu na samu kai na a cikin harkar finafinai, musamman namu na Arewa da ake kira da Kannywood,” inji ta.
To, ko me ya ja hankalin Asabe Madaki zuwa shiga harkar fim, musamman idan aka yi la’akari da karatun ta na aikin lauya? Sai ta amsa da cewa: “Gaskiya mutane za su kalli haka, amma dai ko lokacin da na kammala digiri na na biyu a Scotland na dawo gida, na taba aikin lauya, amma a gaskiya tun lokacin da na ke makaranta ma hankali na ya fi karkata ga masana’antar nishadi, don haka daga baya na shiga harkar fim gadan-gadan.
“Koda yake zan iya cewa tun ina makarantar firamare ina cikin kungiyar dirama da kade-kade da kuma wake-wake. Don haka zan iya cewa abin kamar a jini na ya ke; tun ina karama na ke burin na zama ’yar fim.”
Asabe na da wata ka’ida, wadda ta sa ba a ganin ta a finafinai barkatai. A cewar ta, “Ba kowanne fim na ke yi ba, sai wanda na ga ya na da ma’ana kuma ya ke kunshe da sakon da zai isar ga masu kallon sa. Don haka ba wai don ina son na yi fim ba sai kawai na fito a cikin kowanne irin fim. Don haka a yanzu finafinan da na yi wadanda su ka hada da na Turanci da Hausa su ne ‘Sarauniya’ da kuma ‘Gwaska’, na Turanci kuma sun hada da ‘Laraba’s World’, da ‘Queen Amina’ da ‘Make Room’ da ‘Light and Darkness’, sai kuma wanda ka same ni a yanzu ina yi, ‘This is the Way’ na kamfanin Jammaje Production.”
Da mu ka tambaye ta idan ta samu matsala da ta shigo harkar fim, sai Asabe ta ce, “E to, ba zan iya cewa ban fuskanci matsala ba. Matsalar dai da na samu ita ce a fim din Hausa kasancewar ni ba cikakkiyar Bahaushiya ba ce, don haka wasu kalmomi na Hausa su na yi min tsauri sosai wajen furta su. Duk da cewar zan iya rubutawa da kuma karantawa, amma dai wajen furtawa wadansu za su gane ni ba cikakkiyar Bahaushiya ba ce sai dai a yanzu ina kokarin ganin Hausar ta tsaya a baki na, kasancewar ina da burin bayar da gudunmuwa ta ta hanyar finafinan Hausa.”
Kowane mutum ya na da buri da ya ke so ya cimmawa. Ita ma Asabe na da nata a matsayin ta na jarumar fim. Cewa ta yi: “Buri na dai shi ne in taimaka wa al'umma ta ta hanyar finafinai masu ma'ana, kuma ina so na zama fitacciyar jaruma a duniya. Ina da burin na mallaki kamfanin da zai rinka shirya finafinai ya na fitar da su, kuma ina so na rinka taimaka wa mutanen da su ke shiga harkar fim.”
Wato dai watakila nan gaba a samu wata Lupita Nyong’o kenan daga arewacin Nijeriya; kamar yadda jarumar ’yar kasar Kenya ta bulla daga Afrika ta yi fice a duniya, haka Asabe Madaki ke so ita ma ta yi kenan. To Allah ba ta sa’a, amin.
To me za ta ce kan yadda wasu mutane su ke kallon ’yan fim din Hausa a matsayin masu bata tarbiyya? Lokacin da ta yanke shawarar shigowa cikin harkar fim ta samu kalubale a gidan su sakamakon wannan ganin da ake yi wa ’yan fim?
Amsar Asabe: “Zan iya cewa na samu, domin kuw matsalar farko da na samu a wajen mahaifi na na samu, inda ya ke ganin shi dai na tsaya na kammala karatu na domin ko lokacin da ina jami’a akwai wasu kamfanoni da su ka nemi na yi musu aiki, amma a gida sai iyaye na su ka hana ni don su na ganin hakan zai iya shafar karatu na. Amma da na kammala sai ya zama su na ba ni kwarin gwiwa wajen aikin da na ke yi na fim.”
Abin da ya fi bada mamaki game da Asabe shi ne kasancewar ta jarumar finafinan Hausa da na Turanci. Ko yaya ta ke kallon kan ta a haka?
“To abu ne mai sauki, musamman ma a matsayi na na wadda na ke so na bayar da tawa gudunmuwar domin ci-gaban yanki na na Arewa ta hanyar finafinai,” inji jarumar.
Fim din ‘This is the Way’ aikin sa na Hausa ne, amma da Turanci ake yin sa. Yaya ’yar was an za ta kwatanta shi da sauran finafinan da ta yi? Sai ta ce: “To gaskiya wannan fim din fim ne da ya fita da wasu muhimman darusa a cikin sa wanda mutane ba su san su ba. Idan na ce ba a san su ba, ina nufin wadanda za su kalle shi da kuma yaren da aka yi shi. Ka ga shi labarin al'adar Hausa ne da mutanen Arewa, sai aka yi fim din da harshen Turanci. To ko ka ga ba Hausawa ba ne za su kalle shi, wasu al'umma ne da ba su san al'adar Hausa da mutanen Arewa ba za su gani. To ka ga wannan zai isar da sakon al'adar mu zuwa wata kasa da ba su san mu ba. Za su ga al'adun mu masu kyau da irin yadda mu ke gudanar da rayuwar mu. Don haka shi wannan fim din 'This is the Way' zai samar da fahimtar juna ga sauran al'umar mu da su ke ganin kamar ba mu waye ba ko ba mu iya Turanci ba. Yanzu idan ka duba fim din ‘There is a Way’, wanda shi ma an fitar da shi ya shiga kasuwa, ya bayar da ma’ana sosai wanda ina ganin hakan ce ta sa shi Kabiru Musa Jammaje ya samu karfin gwiwar da ya kara fito da fim din ‘Light and Darkness’ da kuma wannan da ake yi a yanzu, ‘This is the Way’.
Me ya fi burge jarumar a cikin harkar fim?
Asabe: “To abin da ya fi burge ni shi ne na ga an yi fim mai ma’ana da kuma isar da sako. Shi ya sa ma na ke jinjina wa Kabiru Musa Jammaje da kuma kamfanin sa, Jammaje Production, da ya ke fitar da finafinai na Hausa amma da yaren Turanci, domin kuwa wadannan finafinai da wadanda zai fito da su nan gaba su ne za su cike gibin da ya ke tsakanin Nollywood da Kannywood, domin ana ganin kama Turanci ne bambancin mu, to ga shi mu ma mu na yin, don haka duk wanda ya ke ganin Hausa kawai mu ka iya a Kannywood to a yanzu an san mu na yin na Turanci. Kuma finafinan mu za su shiga duniya a rinka ganin al’adun mu na Arewa ta hanyar wadannan finafinai, ‘There is a Way’, ‘Light and Darkness’ da kuma ‘This is the Way’.
Daga karshe, Asabe Madaki ta kira na musamman ga kamfanoni da ke shirya fim a nan Arewa, inda ta ce: “Su yi koyi da wannan furodusa, Kabiru Musa Jammaje, wajen shirya fim mai dauke da al’adun mutanen Arewa kuma da harshen Turanci, don ta haka ne za a rinka sanin al’adun mu da kuma yadda mu ke gudanar da rayuwar mu ba tare da wasu su na bada labarin mu ba yadda mu ke ba.”
©mujallarFim
Comments
Post a Comment