Dandalin Kannywood: Abunda na sa gaba bayan daina fitowa a fim – Sadiya Gyale -,,




Shahararriyar jarumar nan ta Kannywood wacce aka dama da ita a lokutan baya, Sadiya Muhammad Gyale ta yi tsokaci akan abunda ta sa a gaba bayan barinta masana’antar ta shirya fina-finai.
A cewar jarumar ta kama sana’a ne gadan-gadan, inda ta ke saida kayayyaki daban-daban.
Sadiya tace tana saida kayan mata, na maza dama kayan noma domin tafiyar da al’amuranta na yau da kullun.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wani hira da tayi da jaridar Leadership Hausa.

Da aka tambayeta kan batun aure, kyakyawar jarumar tace Insha Allah suna ta addu’a, Allah Ya kawo miji nagari mafi alheri.
A baya Majiyarmu ta kawo cewa tsohon mijin shahararriyar jarumar nan ta Kannywood, Sadiya Gyale wato Alhaji Abubakar Muhammad ya amsa kiran mahallicin sa.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15