Jama'a ga fa Hajiya Zainab, tsohuwar matar Dangote
- Hajiya Zainar, tshohuwar matar Dangote da ta fito a bainar jama'a karo na farko
- Hajiya Zainab itace mahaifiyar Amarya Fatima Dangote da ta yi aure satin da ya wuce
Tabbas shahararren mai kudin nan na daya a dukkan nahiyar Afrika dan asalin garin Kano, Alhaji Aliko Dangote mutum ne mai matukar kankan da kai da kuma kokarin boye rayuwar iyalin sa, hakan ne ma ya sanya ba kowa ne yasan ya rayuwar ta su ta ke ba.
Sai dai daman Hausawa na cewa ranar wanka, ba'a boyon cibi don kuwa yanzu bayanai da ya wa sun fita a bainar jama'a inda aka fahimci cewa shi Dangote din ya taba yin aure a baya, ya kuma rabu da matar ta sa watau mahaifiyar amarya Fatima Dangote kenan da ta yi aure a kwanan baya.
Majiyarmu ta samu cewa a wurin bikin ne ma jama'a suka fara ganin tsohuwar matar ta sa mai suna Hajiya Zainab a inda ta ke gaba-gaba wajen shirin bukukuwan da aka gudanar.
Yawancin mutane dai da sun ga mahaifiyar amaryar za su iya fahimtar hakan ko ba tare da tambaya ba domin irin kamar da suke yi sosai.
A baya ma dai mun kawo maku cewa mijin Fatima din Jamilu shine babban da ga mahaifin sa, tsohon shugaban 'yan Sanda Muhammad Dikko Abubakar, wanda yanzu haka an fara shagalin biki sa da amaryar ta sa.
Shi dai Jamilu matashin mai kudi ne kuma yana da sunan gayu da ake kiran sa dashi a cikin abokan sa wato 'Jamboy' wanda kuma hakan ne yake rubuce a jikin lambar motocin sa na alfarma da.
-Naijhausa
Comments
Post a Comment