Kowa ma ya sani wallahi miliyan 50 Atiku ya bani – Fati Mohammed ga magoya bayan Buhari





Tsohuwar shahararriyar jarumar kamfanin shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Fati Mohammed tayi raddi ga magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ta bayyana cewa babu makawa miliyan 50 tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bata domin yi masa kamfen.

Inda tace duk masu zage-zage wanene ya ji shigar kudi a asusun sa. Ta kuma ce me zaa yi da Buhari da baya bad a ko sisi.

Kowa ma ya sani wallahi miliyan 50 Atiku ya bani – Fati Mohammed ga magoya bayan Buhari
Ta wallafa a shafinta kamar haka: “Kowa ma ya sani wallahi miliyan Hamsin (N50 Million) Atiku ya bani.

“Duk masu zage zage waye ya ji nalert irin nawa.

“Me ake yi da Buhari ko sisi baku samu wajen shi.
“Don Allah ko ku ne kuka ji wannan alert in zaku biye wa wani Buhari?

Naij hausa

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15