Nura M.Inuwa ya yaba ma sauran abokan sana'ar sa na masana'antar nishadantarwa bisa irin jajircewa da suke yi wajen fitar da kayatattun wakoki masu cike da basira
Hazikin mawaki mai zazzakar murna Nura M.Inuwa yana mai jinjina ma sauran mawaka bisa yanayin basirar su wajen fitar da waka.
Mawakin yace yafi jin dadin sauraron wakokin sauran mawaka fiye da tashi kuma ya kan siya wakokin su indai ya ci karo dasu ba tare da zabi ba.
Zakin waka wanda ya dawo da kasa mai tsarki kwana nan inda ya tafi yin aikin Umrah, yayi wannan bayanin a wata sako da ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumunta ta Instagram ranar laraba 18 ga watan Afrilu.
Nura M.Inuwa ya yaba ma sauran abokan sana'ar sa na masana'antar nishadantarwa bisa irin jajircewa da suke yi wajen fitar da kayatattun wakoki masu cike da basira.
Mawakin yace ya kan yi mamakin yadda wasu mawakan ke sanya zance wanda ko kwararrun malaman adabin harshen idan sunji sai sun jinjina ma mawakin.
"Nafi jin dadin sauraron wakokin mawaka yan uwana
fiye da nawa, kuma nakan saurari ta kowa ne ba zaba nake ba,koda yau mutum ya fara waka indai naci karo da ita zansa kudina na saya, da haka nake gane irin hikimomin da ALLAH ya mana daban daban.
kowa da irin wacce aka bashi,da haka kuma nake dada samun damar jinjinawa duk wanda yake da baiwar yin wakar saka makon kokarin sa, sai dai akwai na wanda suke kulle mini kaina naita mamakin yadda suke shiga suke fita suna saka zance wanda ko prof ne yaji sai ya jinjina,sannan ina amfani da wannan damar wajan gane irin yanayin da masoyan mu suke shiga lokacin da suke sauraron mu,wata wakar tana kashe mini jiki naji kamar nayi kuka,wata tasani tunanin makoma ta,wata ta sani tunanin shi kansa mai wakar,dan wani sakon shi kadai yake iya fahimta.
Ya kara da yi ma dinbim masu bibiyar wakokin su addua na Allah ya cigaba da kara soyayya da fahimtar sakonnin da suke fitarwa inda yake cewa "ALLAH ya barmu daku".
Comments
Post a Comment