Dandalin Kannywood: Jaruma Rahama Sadau ta yi wa masu sha'war yin fim nasiha mai ratsa zuciya




Fitacciyar jarumar dai ta bayyana hakan ne yayin da take fira da kamfanin dillacin labarai na Najeriya a wani lokaci a baya a garin Abuja, babban birnin tarayya.

naij ta samu cewa jarumar ta bayyana cewa ga dukkan masu so suyi fice a sana'ar fim din ya zama dole gare su da su jajirce su kuma dage domin cimma burin su. Da take tsokaci game da irin kalubalen da take fuskanta, jarumar ta bayyana cewa dukkan mai rai daman dole ne ya fuskanci kalubale a rayuwar sa. Daga karshe kuma jarumar ta sha alwashin cigaba da shirya kayatattun fina-finai domin nishadantar da dumbin masoyan ta a ciki da wajen Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15