Innalillahi wa inna ilaihirajiun Allah ya yi wa Khalifa Isyaka Rabi'u rasuwa




Allah ya yi wa Shugaban Darikar Tijjaniya a Najeriya Kahlifa Isyaka Rabi'u, rasuwsa, kamar yadda daya daga cikin 'ya'yansa ya shaida wa BBC.

Daya daga cikin 'ya'yan marigayin ya shaida wa BBC cewa ya rasu ne a wani asibiti a birnin Landan na Ingila a yammacin ranar Talata.

Marigayin, wanda ya sha fama da rashin lafiya a 'yan kwanakin nan, ya rasu ne yana da shekara 90 a duniya.
Baya ga malantaka, marigayin kuma hamshakin dan kasuwa ne wanda ya yi fice a fagen kasuwanci a Najeriya.
Bayanai sun za a yi janazar marigayin da zarar gawarsa ta iso Najeriya daga birnin Landan, inda ya rasu.
Ya rasu ya bar mata hudu da 'ya'ya 42 da kuma jikoki da dama cikinsu har da Alhaji Abdussamad Isyaka Rab'iu, wanda shi ne shugaban hadakar kamfanin BUA.

Comments

Popular posts from this blog

BRIEF BIOGRAPHY OF SHEIKH IBRAHIM AHMAD MAQARY, IMAM OF NATIONAL MOSQUE ABUJA

Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Karanta cikakken tarihin sa

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.