Jaruma Rahama SadauTauraruwar Kannywood ta samu kyautar Jarumar Jarumai Na Shekara



Abun farin ciki ya kara samuwa game da basirar Jaruma Rahama Sadau inda jaridar Leadership ta karrama ta da kyautar jarumar jaruman shekara.
A bikin karrama fitattun yan Njieriya da suka taka rawar gani wajen cigaban kasar da aka gudanar a garin Abuja daren ranar alhamis 24 ga watan Mayu ta samu kyautar.

Kasancewar tana kasar Cyprus inda take karatu, tauraruwar masana'antar kannywood ta samu wakilcin jarumi Uzee Usman wanda ya amshi kyautar a madadin ta.



kamar yadda ta wallafa a shafin ta tare da hoton lambar yabon, Rahama Sadau ta nuna farin cikin ta da samun kyautar bayan an hada ta gasa da wasu fitattun jarumai.

Tayi ma dinbim masoyan ta godiya bisa goyon bayan da suke bata na yau da kullum wanda dashi take takama.


Daga karshe tayi ma jaridar Leadership godiya ta karramawar da suka bata tare da Uzee wanda ya amshi kyuatar a madadin ta.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15