Burin kowace ‘ya mace shi ne ta wayi gari a cikin dakin mijinta musamman idan an kai kan gabar yin auren. A ranar 27 ga Afrilun da ya gabata ne ‘yan fim mata suka yi gangamin zuwa bikin Rahama Isah Sirace wadda ta fito a fim din sirace na Kamfanin Sarauniya fims Kano.
An daura auren da rana bayan sallar Juma’a sai kuma aka dunguma aka je gurin walimar bikin, inda ’yan fim mata suka yi wa amaryar karar bazata. Ko da muka nemi jin ta bakin ita amaryar, ta bayyana farin cikinta da kuma godiya ga daukacin wadanda suka samu damar halartar bikin da kuma wadanda uzuri ya hana su zuwa.
“Assalamu alaikum ‘Yan’uwa Ina mika godiyata gare ku duka da wadanda ba su sami damar zuwa ba da wadanda suka zo ba mu hadu ba suka tafi duk ina wa kowa fatan alheri. Na san na yi lattin zuwa har aka fara bikin ba a jira ni ba har wasu ma suka tafi ban iso ba duk ina neman afuwar kowa da kowa. “An nuna min kara na kuma ji dadi sosai, zan mika jinjinata ga babbar aminiyata Sadiya Gyale ta faranta min matuka sosai abun da ta yi min ina mata adu’ar ita ma Allah ya ba ta wanda zai saka mata fiye da hakan. Na gode wa anty Halisa, na gode wa Anty Wasila da kika taso daga Kaduna kika zo bikina a Kano, ina yi wa Alhaji Afakallahu shugaban hukumar fim ta Kano godiya, Umar Gombe, Mama Mai Sanafahna, da iyayena da ‘yan’uwana dukansu, in har na ce zan cigaba da Lissafo Sunayen mutane sai an cika shafuka goma don kuwa biyar ya yi mana kadan. Ina godiya ga Fati Ladan don ita ma ta nuna min soyyayar hakika a wanan bikin nawa, Dan Allah a taya mu da addu’a Allah ya zaunar da mu lafiya da mazajenmu. Sanan kuma ina rokon duk wadda na bata wa ya yafe min nima na yafe masa Allah ya yafe mana gaba dayanmu, kuma ina yi wa uwar dakina ta musamman godiya. Wato Shafa Wali, Allah ya daukaka ta fiye da yadda take amin, kuma ina godiya ga ’yan makarantarmu Hausawa ‘Model’ sun zo sun taya ni farin ciki, Sun yi anko sun zo sun taya ni farin ciki.
Idan Mai karatu zai iya tunawa Rahma Hassan ta yi aure a watan Janairun 2017. Ta auri masoyinta Ambasada Usman el-Kudan. An yi bukukuwan a Suleja da Abuja da kuma Kaduna, biki ne wadda an dade ba’a yi irin sa ba a tarihin ‘yan fim, don kusan duk wata ‘yar fim mai ji da kanta da dan fim Mai ji da kansa ya halarci wanan taroruka da suka shirya.
Bikin ya yi kyau sosai yanzu bayan shekara da yin, Allah ya azurta su da diya wacce aka rada wa suna Ummu Salma wadda suka sa mata lakabin ‘Islam’. Rahma, wato da ita ma lakabinta ya koma ‘Mummy Islam’ ta haihu a Suleja, inda daga bisani suka dawo Kaduna gidan mijinta suka shirya gagarimin liyafar Suna Mai kyau na gani na fada. ‘Yan fim da abokan arziki sun rakashe sosai a wanan bikin Suna na Islam.
Shafin Taurarin Nishadi ya nemi jin ta bakin Angon Karni da Amaryar Karni (Maijego) kan karuwar da suka samu ta haihuwa inda suka bayyana farin cikinsu da kuma godiya ga Allah Madaukakin Sarkin kan abin da suka samu. Ga abin da suka ce:
“Assalamu alaikum waramatullahi ta’ala wa bara katahu. Sunana Rahma Hassan a yanzu kuma Mrs Usman el-Kudan. Ina son amfani da wanan daman in godewa Allah da ya azurta mu da babban kyauta ta kyakyawan yarinya wadda muka rada mata Suna Ummu Salma kuma muke kiranta da Islam, Ina son mika godiyata gareku da addu’o’in da kuke ta mana tunda muka yi aure kuma ba ku yanke ba har yanzu kuna yi mana ko bayan arzikin haihuwa da Allah ya bamu, Ina mika godiya mara adadi ga wadanda ba su sami daman zuwa ba amma sun aiko mana da sakonin ‘tedt messages’ da kira, Mun gode sosai Allah subhanahu wata’Allah ya saka ma kowa da kowa da alheri.
“Wanan sakon daga gareni ne da mijina Daddy Islam, sanan wadanda kuma suka sami daman zuwa Mun gode sosai da lokacin ku da ku ka ware kuka zo kuka taya mu murnar wanan rana. Allah Ubangiji ya saka maku da alherisa. Daddy Islam yana mika godiyarsa Allah ya saka maku da alheri. Masu iyali Allah ya raya mana, masu neman haihuwa Allah ya basu, Allah ya biya wa kowa bukatarsa ta alheri amin ya Rabbi. Allah ya sa yaran mu su zaman abin alfahari a duniya baki daya, godiya ta ba za ta isa ba in har godiyar zan yi, don ban da adadin godiyar da zan furta maku a nan. Allah Ubangiji ya bar mana zumunci, ina yiwa kowa da kowa fatan alheri, na gode”.
Comments
Post a Comment