Dandalin Kannywood: Hassan Giggs da Muhibbat Abdulsalam sun cika shekara 10 da aure



Fitaccen mai bada umarni a kamfanin shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Hassan Giggs, ya kasance cikin murna yayinda suka cika shekaru 10 da shi da matarsa kuma tsohuwar jarumar fim, Muhibbat Abdulsalam.
Diraktan ya zamo daya daga cikin manyan masu bada umarni a masana’antar sanna kuma matar tasa na cikin jarumai mata da suka takar rawar gani a masana’antar cikin shekarun baya.
Don raya zagayowar ranar auren su, mauratan sun wallafa hotunan su tare da 'ya'yansu a shafukan su na kafafen sada zumunta tare da yi ma Allah godiya bisa yadda kaunar su ya cigaba da daurewa.

Ga sakon da Hassan Giggs ya rubuta bayan wallafa hoton su kamar haka; "Kyauta mafi soyuwa da zaka baiwa yaran ka shine ka so mahaifiyar su. Shekara 10 ba wasa ba, komai sai da yaddar Allah. Alhamdulillah yau mun cika shekarar goma da yin aure ."
Ita ma matar sa bata yi jinkiri ba wajen rubuta sako mai inganta kauna. Tayi ma mijinta kirari.

Comments

Popular posts from this blog

BRIEF BIOGRAPHY OF SHEIKH IBRAHIM AHMAD MAQARY, IMAM OF NATIONAL MOSQUE ABUJA

Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Karanta cikakken tarihin sa

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.