Ababe 5 da ya kamata ku sani game da shirin Fim din da gwamnan jihar Bauchi zai bayyana a ciki




Kamar yadda gama garin mutane suka sani cewa, dandalan sada zumunta sun dimauce cikin musayar zantuttuka da ra'ayoyi dangane da shirin fim din nan mai taken “Up North” , da gwamanan jihar Bauchi, Muhammad Abubakar, zai fito a cikin sa.
Ko shakka babu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, ma'abota dandalan sada zumunta sun yi musayar ra'ayoyi dangane da wannan shawara da gwamnan jihar Bauchi ya yanke ta fitowa cikin shirin, inda mafi akasarin su ke ganin babu dacewa idan an duba lamarin ta mahangar al'adar mu da kuma kasancewar sa bambarakwai ga kowane gwamna dake kan mulki.

Majiyarmu ta fahimci cewa, wannan shirin fim zai hadar da mawaka da fitattun jarumai na Kannywood da kuma Nollywood irin su; Kanayo O. Kanayo, Banky W, TBoss, Michelle Dede, Akin Lewis, Rahama Sadau da kuma Sa'eed Muhammad.

Daya daga cikin ja gaban masu shirya fim din na Up North, Editi Effiong ya bayyana cewa, gwamnan na Bauchi ba wai kawai zai fito a cikin shirin bane zai kuma tabbatar da ganin shirin ya samu daukaka da nasara.
Ga wasu jerin ababe 5 da ya kamata ku sani game da fim din wanda gwamnan Bauchi zai fito a cikin sa:

1. Shiryawa: Kamfanin shirya fina-finai na Inkblot Productions tare da hadaka ta kamfanin Anakle Films na reshen Anakle Digital su zasu dauki nauyin shirya wannan fim na Up North .
2. Bayar da Umarni: Fitaccen mai bayar da umarnin nan, Tope Oshin, shine zai gudanar da al'amurran wannan sabon shiri.
3. Ranar Fitowar sa: Kawowa yanzu ba a kayyade ainihin ranar fitowar wannan shiri ba, sai dai za a fara haska shi a gidajen Silima dake fadin kasar nan a watan Dasumba, inda ake sa ran gwamnoni da Sarakunan gargajiya za su halarta.
4. Wurin haska shirin: Za a haska wannan shiri ne a jihar Bauchi da kuma Legas, sai dai tun daga taken sa ka iya cewa mafi akasarin wurin haska shi zai kasance yankin Arewa.
5. Shirin Up North shine fim na farko da Dandalin Nollywood zai haskaka gwamna mai ci a cikin sa tare da Sarkin gargajiya guda daya a tarihin kasar nan.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15