Babu Wanda Yasan Waye Zaici Zaben 2019 - Inji Halima Atete





Halima Atete wacce aka saba gani a fina finan Hausa ta banbanta da Halima Atete a zahiri. A mintocin da muka zauna da ita mun gane cewa mutun ce mai saukin kai, da son jama’a, da kuma hangen nesa.
Kun san a fim, mutum yana kokarin sajewa ne da yin kwaikwayon halayen dan wasan da yake wakilta domin ya fito da asalin dabi’an wannan dan wasan dake cikin labarin fim. Wannan shine yake nuna shahara da tayi wajen fim, domin ko a mene ta fito tana yin sa ne da kwarewa.
Bata nuna bacin rai ko ta daga kai ba. Bata nuna isa ko takama ba a iyakacin zaman da muka yi da ita ba. Ta bamu goyon baya dari bisa dari.
Ita dai Halima Atete ‘yar Jihar Borno ce. Ta fito a fina finai daban wadan suka kunsa ire iren su Maza Da Mata, Dakin Amarya, Kona Gari, Hannu da Hannu, Asalina, da dai sauran su.
A zaman da muka yi da ita, mun tattauna akan abubuwa daban daban, wanda mai karatu zai biyo mu ya karanta su kamar haka:
Dan Jarida: Barka da war haka.
HALIMA ATETE: Barkan mu dai.
Dan Jarida: A matsayin ki na ‘yar film kuma sananniya, shahararriya wanda kowa ya sani, har i’zuwa yanzu akwai wani nasara da kike nema wanda baki samu ba?
HALIMA ATETE : Assalamu Alaikum. Toh ai kinsan kogi ma bai ki a kara masa ba ko? Alhamdulillahi, nasarori duk wanda ya kamata ace mutun ya samu a cikin sana’ar sa ko akan sana’ar sa Allah ya bani. Ba abinda zance sai dai, mun gode wa Allah, Allah kuma ya kara mana.
Dan Jarida: Kaman ranakun da baki wajen fim, ko kuma baki da aiki na fim, kaman me da me kike yi?
HALIMA ATETE: Kawai dadi nake ji. In kwanta a kan kujera ta a gida ina chatting, ina dan wasu abubuwa. Ina dan wayoyi na da baza a rasa ba. In kuma na gama, in fita inje in ci Tsire.
Saboda ina son ci Tsire da Coke duk sanda nake cikin walwala. Kawai inje in fita in dawo gida.
Dan Jarida: Shin kina siyasa kuwa?
HALIMA ATETE: Siyasa idan ya kama dole inyi, ko kuma ince ina yi.
Dan Jarida: A shekarar zabe ta dubu buyu da sha tara(2019), ya ya kike ganin siyasar kasan zata kasance?
HALIMA ATETE: Har kullum dai mu talakawa ya kamata mu dinga duba shugabanni masu adalci. Amma kafin nan ya kamata muma mu dinga tsarkake zukatan mu, sannan Allah ya bamu shugabanni na gari.
Siyasar shekara ta dubu biyu da sha tara kamar mace ce mai ciki, babu wanda yasan abinda zata haifar sai lokacin yayi. Addua’r mu ita ce, Allah yayi mana zabi wanda yafi alheri ga mu ‘yan Najeriya.
Dan Jarida: Amin Amin . Toh me zaki ce akan gidauniyar da Mallam Yahaya ya bude?
HALIMA ATETE: Eh abinda zance shine; muna rokon masu hanu da shuni, da en kasuwa, en gwamnati, da duk wanda ke da halin taimakawa, ya fito ya taimaka. Duk wanda ya taimaka ma wanda bashi da shi, Allah shima zai taimaka masa. Mallam Yahaya ma a haka yake taimakawa.
Shin mai zai hana su manyan mu masu hanu da shuni da kuma gwamnati su kara taimaka wa al’umma tunda suna rike da madafan iko. Masu kananan sana’oi suma sunada rawan da zasu taka.
Mun san kila basu da shi a wadace, amma kuma daga kadan din da suke da shi zasu iya bada nasu gudummuwar. Har wa kullum idan mutum ya taimaka da tsarkakacciyar zuciya kinga sai Allah ya kara buda masa. Kada mu manta fa duk abinda mutum ya samu a nan duniya, sai Allah ya tambaye mu yanda muka samu kuma da yanda muka batar da su wannan dukiyoyin.
Ni shawara ta a gare su shine; su fito su dan kara taimaka wa masu neman taimako.
Dan Jarida : Daga karshe akwai sako ta musamman da zaki bayar zuwa ga masoyan ki?
HALIMA ATETE: Ni masoya na har kullum ba abinda nake cewa sai dai karin godiya gare su. Kuma Allah Ubangiji ya kara hada zukatan mu. Allah Ubangiji ya sa duk inda muka hadu mu zama tamkar tsintsiya madaurin ki daya.
Dan Jarida: Toh mun gode sosai.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15