Ko ina labarin jarumi Dharmendra na Indiya?




Dharmendra na daya daga cikin jaruman fina-finan kasar Indiya da suka yi fice saboda irin rawar da suka taka.
Jarumi ne wanda ya yi suna wajen fina-finan fada, da jarumta da kuma na barkwanci.
An haife shi a ranar 8 ga watan Disambar 1935, kusan shekara 83 ke nan.
Sunansa na ainihi Dharam Singh Deol, an kuma an haife shi a kauyen Nasrali da ke gundumar Ludhiana a yankin Punjab.
Dharmendra bai yi karatu mai zurfi ba, kuma an masa aure da wuri, domin tun yana da shekara 19 a duniya iyayensa suka aura masa Parkash Kaur a shekarar 1954.
sun haifi 'ya'ya biyu maza, wato Sunny Deol da Bobby Deol.
Yaushe ya fara fitowa a fim
Dharmendra ya fara fim ne tun zamanin fina-finai marasa launi, ma'ana tun zamanin hoton bidiyo fari da baki.
Ya fara fim ne a shekarar 1960, in da ya fito a matsayin mataimakin jarumi, wato supporting actor a fim din Dil Bhi Tera Hum Bhi Tere.
Daga nan ne kuma ya ci gaba da fitowa a fina-finai.
Sai dai kuma fina-finansa na shekarun 1970, sun fi haskaka shi da kuma karbuwa.
Sanannun fina-finansa sun hadar da Sholay da
Dharam Veer da Charas da Ghazab da Hukumat
da Dream Girl da The burning train da Seeta aur Geeta .



Akwai jituwa tsakanin Dharmendra da Amita Bachchan sosai, saboda yawancin fina-finan da suka yi tare sun samu karbuwa sosai a wajen 'yan kallo.
Fina-finansu tare sun hadar da Ram Balram da
Sholay da Chupke Chupke da Chala Murari Hero Banne da dai makamantansu.
Duk da yake Dharam ya girmi Amita, akwai kyakkyawar alaka tsakaninsu har yanzu, kuma suna ganin girman juna.
A kalla Dharam ya yi fina-finai 204 a tsawon rayuwarsa.
To sai dai kuma duk da fitattun fina-finan da ya yi, bai taba samun kyautar gwarzon jarumai ba wato best actor award.
Yawanci dai maza na son fina-finansa saboda akwai fada, ba kasafai ya fiye fina-finan soyayya ba.
Ko Dharamendra na fitowa a fina-finai har yanzu?
Dharam na fitowa a fina-finai har yanzu, amma jefi-jefi.
Ba kamar Amita Bachchan ba, Dharam baya fitowa a fina-finai sosai, koda yake akwai fim din sa Yamla Pagna Deewana Phir Se da zai fito ranar 31 ga watan Augustan 2018.
Fim din na su ne, sun kuma fito tare da 'ya'yansa Sunny da Bobby Deol.
Me ya ke yi a yanzu haka?
A yanzu haka babu abinda Dharam ke bukata illa ya rinka shakatawa a katafaren gidan gonarsa da ke Lonawala.
Ya kayata gidan gonar, shi ya sa ya ke zuwa don ya huta.
Kazalika Dharam mijin mata biyu ne, domin bayan matarsa ta fari da suka yi aure tun da kuruciya, daga bisani ya auri jaruma Hema Mailini a shekarar 1979, bayan ya kasa jarumai kamar Shatrungan Sinha da Manoj Kumar a takarar nemanta.
Su ma 'ya'yansu biyu amma mata wato Esha Deol da Ahana Deol.
Esha ita ma jaruma ce, domin ta taba yin fina-finai kafin ta yi aure, amma Ahana ba ta taba yin fim ba, kuma ita ma tayi aure



Abinda ya ke daure wa jama'a da dama kai shi ne, ya aka yi ya ke da mata biyu?
Bayanin shi ne, lokacin da suka fahimci juna shi da Hema har suka so aurar juna, addininsu na Hindu bai basu damar auren fiye da mace guda ba, don haka sai suka musulunta suka yi aure, kasancewar addinin musulunci ya bayar da damar auran mace fiye da guda.
Dharamendra dai duk da shekarunsa ba shi da wata cuta da ke damunsa, kuma akwai sa'anninsa da dama wasu ma ya girme su da ya fi su kyan gani.
Kuma shi na kowa ne, shi ya sa jaruman da ke tashe a yanzu, ke bashi girmansa.
Sannan kuma a baya ya taba siyasa, don har mukami ya rike a yankinsu.


Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15