Tirkashi: Zpretty ta caccaki 'yan soshiyal midiya
Matashiyar jarumar masana’antar Kannywood , Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zpretty ta caccaki ma’abota tsegumi a kafafen sada zumuntar zamani - Jarumar ta wallafa bidiyo a shafinta na Instagram ne inda ta ke magana a kan masu bata wa jaruman masana’antar suna - Ta yi gargadin cewa, zata iya daukar mataki a kan duk wanda ta kama da laifin bibiyar lamurranta tare da bata mata suna Matashiyar jarumar masana’antar Kannywood, Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zpretty ta caccaki ma’abota amfani da kafafen sadarwa ta zamani. A wani bidiyo da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, ta yi suka ga wadanda suka kware wajen bibiyar lamuranta da na sauran jarumai abokanan sana'arta. Wadanda daga zarar sun ga jarumi ko jaruma ta wallafa sabon hoto, zasu fara yadawa tare da tsokaci a kai. Jarumar ta yi kausasan kalamai na musamman ga masu wallafa bayanai a dandalin YouTube, inda ta ce mafi yawansu basu da aikin yi face shirya karya da gulma, don batawa jaruman masana’antar Kannywoo