Hadarin jirgin ruwa mai muni yaci mutane 17 yan kasuwa a jihar Kebbi
Dukan iccen keda wuya, sai jirgin ruwan ya dare gida biyu, hakan ya sanya jirgin nutsewa, inda mutane goma sha bakwai suka ce ga garinku nan, sa’annan mutane uku ba’a gansu ba sama ko kasa.

A nasa bangaren, shugaban karamar hukumar Yawuri, Musa Muhammad Yawuri ya bayyana alhininsa da faruwar wannan mummunan lamari, inda tare da kansilolinsa suka kai ziyarar ta’aziyya zuwa inda lamarin ya auku. A yayin ziyarar tasa, shugaban karamar hukumar ya bada umarnin a cigaba da neman sauran jama’a da ruwan yayi awon gaba dasu, sa’annan ya bada umarnina a garzaya da sauran gawawwakin zuwa babban Asibitin Yawuri.
Comments
Post a Comment