Ban san adadin dukiyar da na mallaka ba -Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya
shaida wa BBC cewa bai san adadin dukiyar da ya mallaka
ba, amma ya ce ya samu kashi 95% na dukiyar ne kafin ya
shiga siyasa.
Sai dai bayanan da kotun kula da da'ar ma'aikata ta fitar sun nuna
cewa ya mallaki dimbin dukiya da kadarori a ciki da wajen kasar.
Sanata Saraki na fuskantar shari'a kan zargin yin karya a kadarorin
da ya bayyana kafin ya zama gwamnan jihar Kwara a shekarar
2003, lamarin da ya musanta.
Ya shaida wa Naziru Mikailu cewa akwai cin hanci a Najeriya,
amma ya ce ya tara dukiyarsa ne saboda daukakar da Allah ya yi
wa iyayensa da kuma kwazonsa.
Sannan ya ce yana da kwarin gwiwa cewa zai wanke kansa a
shari'ar da ake yi masa, domin cigaba da zama a kan karagar
mulki.
Tsohon gwamnan na jihar kwara ya kuma bai taba kaucewa biyan
haraji ba - zargin da ya taso a takardun bincike na masu kaucewa
biyan haraji wato Panama Papers.
An ambaci sunan matarsa a bayanan inda aka zarge ta yin rijistar
wani kamfani a kasar waje domin sayen gida a birnin London.
Wasu daga cikin tambayoyin da Naziru Mikailu ya yi wa
Saraki
NAZIRU: An dade ana magana a kan batun cin hanci da rashawa,
ko ka amince cewa cin hanci yayi wa Najeriya katutu?
SARAKI: Hankalina ya koma ne ga batun cewa hakika akwai
matsalolin da suka kamata a warware, amma ba zan yi ta
jaddada hakan ba. Saboda ni ma ina tallata kasata ne, don in
sami shigowar 'yan kasuwa masu zuba jari. Shi ya sa ya zama
wajibi in samar da wani yanayi da ya dace wanda zai karfafa
hakan, don in babu hakan, don gwamnati ita kadai, zai yi wuya
mu sami ci gaban da muke bukata.
NAZIRU: Ko ka ga ana aikata cin hanci a harkokin gwamnati?
SARAKI: Tabbas, akwai matsala, shi ya sa ma muke da aikin sa
ido kan gudanar ayyuka. Kamar sauran wasu kasashen duniya
da dama, mu ma muna da ire-iren wadannan matsaloli. Amma
dai ina ganin mun yi nisa wajen shawo kan matsalar.
NAZIRU: Mutane da dama a kasar nan na yi wa 'yan siyasa kallon
masu kudi - shin kai nawa ka mallaka a rayuwarka?
SARAKI: Ban sani ba.
NAZIRU: Nawa ka bayyana a matsayin kadararka kafin ka shiga
siyasa?
SARAKI: A zamana nan ba na iya tuna alkaluman da na
gabatar.
NAZIRU: Wannan na nufin cewa makudan kudade ne ke nan?
SARAKI: Ba na jin laifi ne a ko'ina a ko dai ka yi aiki tukuru ko
kuma Allah Ya albarkace ka, ka sami arziki. Amma dai abin da
nake gani muhimmi shi ne sadaukarwarka ta yi wa jama'a aiki.
NAZIRU: Ta yaya ka mallaki wannan dinbin dunkiya?
SARAKI: Na fito ne daga iyalin da Allah Ya yi wa albarka ta
arziki. Iyayena sun samu dama a rayuwarsu, kuma kafin nan
ma na yi fadi-tashi a harkokin kasuwanci. Ina ganin na yi aiki
da gumina, na mallaki duk abin da nake da shi. Je ka duba
dukiyata, kashi casa'in da biyar cikin na mallake ta ne tun kafin
in shiga gwam nati.
NAZIRU: Ka yi magana akan tara kudaden shiga da karbar haraji,
amma sai ga shi an ambato daya daga cikin iyalanka a takardun
bincike na masu kaucewa biyan haraji wato Panama Papers?
SARAKI: Wannan batu ne na kafa wani kamfani, amma babu
wani da ake da alaka da batun biyan haraji.
NAZIRU: To amma mai yasa aka kafa kamfanin?
SARAKI: An yi hakan ne bisa shawarwarin lauyoyi, saboda za a
sayi wata kadara, kuma ita ce shawarar da aka bayar a wancan
lokacin. Ba wai kamfani ne da muka kafa da kanmu ba, a'a,
lauyoyi ne suka kafa, kuma a iya saninmu babu wata doka da
aka keta.
NAZIRU: Kana fuskantar shari'a a yanzu haka inda ake zarginka da
yin karya wurin bayyana kadarorinka?
SARAKI: Wannan haka yake, kuma ana ci gaba da wannan
shari'a.
NAZIRU: Ko ka bayyana wata kadara da ba ka mallaka ba?
SARAKI: Kamar yadda na dade ina fada game da wannan
shari'a, zan wanke kaina, zan tabbatar da cewa ban aikata laifi
ba. Wadannan takardu ne da na cike tun shekaru sha uku da
suka wuce, amma ba a taso da batun ba, sai a watan Agusta
bayan da na zama shugaban majalisar dattawa. Da ace akwai
wani kuskure a ciki, da kamata ya yi kotun kula da da'ar
ma'aikatan ta yi magana a kai, amma ba su yi ba. Don haka,
kamar yadda na fada, ina da kwaarin gwiwar wanke kaina,
domin babu wani laifi da na aikata.
Comments
Post a Comment