HAKKIN MUSULMI AKAN DAN UWANSA MUSULMI. 38(Sheikh Daurawa)
HAKKIN MUSULMI AKAN
DAN UWANSA MUSULMI. 38
1 Yayi masa sallama idan
sun hadu
2 Yayi masa murmushi da
faraa
3, Ya mika masa hannu su
gaisa
4, Idan ya kira shi ya amsa
5, Idan BASHI da lafiya
yaje ya dubu shi.
6, Idan ana binsa bashi ya
taimaka masa wajan biya
7, Ya dinka kyautata atata
masa zato
8, Ya zauna dashi lafiya.
9, Ya bashi abinki idan
yana Jin yunwa.
10, Ya girmama dattijo
musulmi
11, Ya tausawa yaro
musulmi.
12, Ya cika masa alkawari
idan sunyi alkawari.
13, Yayi masa sulhu Da
wanda suka sami rashin
jituwa.
14, Kada ya dinka tuhumar
musulmi.
15, Ya nema masa alfarma
idan yana da wata bukata
16, Ya dinka girmama
malamai da masu Ilmi
17, Yayi masa addua idan
yayi atshawa
18, Idan ya nemi agajinka
ka agaza masa.
19, Ya dinka yi masa
addua da fatan alkhairi.
20, Kada ya zalunce shi
21, Kada ya tabar dashi
22, Kada ya dinka yi masa
hassada akan wata niima
da Allah yayi masa.
23, Ya girmama shi idan
yazo masa a matsayin
bako.
24, raka janaizar sa. Idan
ya mutu.
25, Ya je kabarinsa domin
ziyara da addua.
26, Ya so masa abinda
yake sowa kansa
27, kada ya cuci musulmi
28, ya zama Mai tawadiu
ga kowa.
29, kada yayi gulmar sa.
Ko yayi masa
annamimanci
30, kada ya kaurace masa
fiye da kwana uku.
31, Ya kyautatawa dan
uwansa musulmi.
32, Kada ya shiga gidansa
sai da izninsa
33, Ya umarceshi da
kyakyawan halaye ya
hanashi mummunan hali.
34, Kada yayi ciniki akan
cikinsa.
35, Kada ya nemi aure
akan auransa.
36. Kada ya dinka yi masa
bincike da bin diddiginsa.
37, ya kubutar dashi idan
yayi rantsuwa.
38, Ya kiyayi mutunci da
dukiya da jini na musulmi.
Comments
Post a Comment